Kwankwaso Ya Hango Nasara a Zaben 2027, Ya Bayyana Shirin da NNPP Ta Yi

Kwankwaso Ya Hango Nasara a Zaben 2027, Ya Bayyana Shirin da NNPP Ta Yi

  • Dan takarar shugaban kasa karkashin NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwanwaso ya ce ya hango nasarar jam'iyyar a zaben 2027
  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP ta yi babban shiri na tunkarar 2027 kuma ba za a barta a baya ba
  • A wata ziyara da ya kai sakatariyar NNPP ta jihar Osun, tsohon gwamnan Kano ya ce jam'iyyar na da kyakkyawar manufa ga talaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Jagoran jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi'u Kwankwaso, ya yi magana kan babban zaben Najeriya na 2027 da ke tafe.

Tsohon gwamnan jihar na Kano ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP za ta taka rawar gani a zaben 2027 domin ta dauki manyan matakai.

Kara karanta wannan

Ighodalo vs Okpebolo: Jigon PDP ya hango wanda zai lashe zaben gwamnan Edo

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan nasarar NNPP a zaben 2027
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana shirin da NNPP ta yi gabanin zaben 2027. Hoto:@KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso ya hango nasarar NNPP

A cewar Kwankwaso, za a karfafa sassan jam’iyyar NNPP na jihohi kafin zabe mai zuwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan lokacin zaben 2027 ya zo, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce ba za a bar NNPP a baya ba, yana mai cewa shirye-shirye sun yi nisa na samun nasararta.

An ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023 ya bayyana hakan ne a Osogbo, babbar birnin Osun a wata ziyara da ya kai sakatariyar jam'iyyar ta jihar.

Wata sanarwa da shugaban NNPP na Osun, Dakta Tosin Odeyemi ya fitar a ranar Juma’a, ta ruwaito Sanata Kwankwaso ya na jaddada hango nasara a zaben 2027.

Kwanwaso ya bayyana shirin NNPP

Sanarwar ta ce Kwankwaso ya samu wakilcin kwamitin mutum uku da suka hada da Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, Dakta Muhammad S. Khalil, da Alhaji Abdusalam Abdulateef a ziyarar.

Kara karanta wannan

"Za mu ceto ku": Kwankwaso ya fadi niyyarsa game da mulki a 2027

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, sanarwar ta ambato Kwankwaso na cewa:

"Rahotanni daban-daban daga Jihohi, musamman Osun, suna ba ni farin ciki a matsayina na jagoran NNPP na kasa. Mun san akwai kalubale a kasar, amma mun yi shiri.
“Ya zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun fahimci cewa shugabanni daban-daban da muke da su suna jefa talauci ne a tsakanin ‘yan kasa da gangan.
“NNPP a matsayinta na jam’iyya ta na da kyakkyawar manufa ga talakawa. Mun fara tara jama’a ta ko ina. A shirye muke mu karfafa sassan jam'iyyar na jihohi.”

Kankwaso ya kara da cewa sun samar da wadatattun ofisoshin jahohin jam'iyyar sannan suna ba su ababen hawa domin saukaka musu zirga-zirga.

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

A wani labarin, mun ruwaito cewa jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Kwankwaso, ya ce shi ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2027.

A yayin kaddamar da sakatariyar NNPP a Katsina, Kwankwaso ya ce jam’iyyar ta shirya karbar ragamar shugabancin kasa, jihohi da sauran mukamai a fadin ƙasar nan zuwa 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.