"Abin da Ya Faru a Zabukan 2015, 2019 da 2023" Inji Shugaban Jam’iyyar PDP

"Abin da Ya Faru a Zabukan 2015, 2019 da 2023" Inji Shugaban Jam’iyyar PDP

  • Umar Iliya Damagum ya ce saken da PDP ta yi a zaben 2015 ya jawo ta zama jam’iyyar hamayya a Najeriya har yau
  • Shugaban PDP na rikon kwaryan ya yi ikirarin Atiku Abubakar ya doke Muhammadu Buhari da suka gwabza a 2019
  • Ambasada Damagum ya na ganin ko a babban zaben 2023, hukumar INEC ta yi magudi ne har jam’iyyar APC ta yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shekaru kusan 10 kenan jam’iyyar APC ta maida PDP ‘yar hamayya a Najeriya, a karon farko a tarihi tun da aka kirkire ta.

Ambasada Umar Iliya Damagum wanda shi ne shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a kasa ya yi bayanin yadda suka canza a yau.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

APC - PDP
Jam'iyyar PDP ba ta yarda APC ta lashe zabukan Najeriya ba Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ya aka yi APC ta doke PDP a 2015?

A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, Umar Iliya Damagum ya bayyana abin da yake tunanin ya jawo masu rashin nasara a 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Galabar APC a kan Goodluck Jonathan a zaben 2015 ta sa PDP ta zama ‘yar adawa, Umar Iliya Damagum ya koka kan rikicin cikin gida.

Yayin da Ummaru Yar’adua ya rasu a 2010, shugaban na PDP ya ce wasu sun ji haushi da shugaba Goodluck Jonathan ya karbi mulki.

Wasu su na ganin tikitin mutanen Arewa ne saboda haka Jonathan daga kudu bai kamata ya karbi mulki ba, wannan rikicin ya ci PDP.

Damagum yake cewa abin takaici PDP ta gaza shawo kan fusatattun ‘ya ‘yanta a lokacin, a karshe aka lahanta jam’iyyar a zaben na 2015.

Kara karanta wannan

"Har da kai a ciki": APC ta caccaki tsohon jigonta kan sukar Buhari da Tinubu

"Mun yi wasa da yiwuwar rasa mulki. Mu na kallo gwamnoni na barin jam’iyya kuma su ka yake mu. Tun daga nan tasirin jam’iyyar ya ragu."

- Umar Iliya Damagum

Jam'iyyar PDP a babban zaben 2019

Duk da haka, Damagum ya ce bayan 2015 tsofaffin gwamnonin da suka yaki PDP sun dawo illa Rotimi Amaechi da ya zama minista.

A zaben 2019, shugaban PDP na rikon kwaryan ya yi ikirarin su ne suka lashe zabe ba Muhammadu Buhari da INEC ta ba nasara ba.

"Mun yi kokari da kyau a zaben nan (2019), duk mun san abin da ya faru bayan nan. INEC tayi dabarar da ta yi, amma na yi imani mun ci zabe."

- Umar Iliya Damagum

Damagum: "PDP ta ci zaben 2023"

Wannan rikicin cikin gidan ne ya bi PDP a zaben 2023, amma duk da haka Ambasada Damagum ya na ganin Bola Tinubu bai ci zabe ba.

Kara karanta wannan

"Ba cire tallafi za a yi ba": Kwankwaso ya fadi tanadinsa kan badakala a bangaren mai

A ra’ayinsa, idan aka duba IRev za a ga PDP ta yi nasara a irinsu Yobe da Borno amma aka ki bayyana sakamakon zaben sai tsakiyar dare.

Ministocin APC da ake bincike

Wasu da suka rike mukaman Ministoci a tsohuwar gwamnati suna da takardu a ICPC da EFCC kamar yadda Legit Hausa ta kawo labari.

ICPC ta waiwayi Dr. Chris Ngige ana binciken kwangilolin NSITF kuma akwai surukin Muhammadu Buhari wanda ake bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng