Zaben Kano: Sani Danja Ya Sha Kaye a Neman Takarar Kujerar Ciyaman karkashin NNPP
- Sani Musa Danja ya sha kaye yayin da aka kammala zaben fitar da gwani na NNPP domin tunkarar zaben kananan hukumomin Kano
- An rahoto cewa Ambasada Yusuf Imam (Ogan Boye) shi ne wanda NNPP ta tsayar a matsayin dan takararta na ciyaman a yankin Nasarawa
- A yayin da Danja ya taya Ogan Boye murna, Legit Hausa ta ji ta bakin wasu daga cikin 'yan Kano kan rashin nasarar da jarumin ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Sani Danja, ya fadi zaben neman takarar kujerar ciyaman karkashin jam'iyyar NNPP a Kano.
An rahoto cewa Sani Danja ya sayi fom din sha'awar neman takarar ciyaman na karamar hukumar Nasarawa, a zaben kananan hukumomin Kano mai zuwa.
Sani Danja ya karbi ƙaddara
A wani bidiyo da Sani Danja ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya kai ziyara ga Ambasada Yusuf Imam (Ogan Boye) wanda NNPP ta tsayar matsayin dan takara.
A cikin bidiyon, an ga Sani Danja tare da Ogan Boye suna gaisawa wanda hakan ke nuna cewa mawakin ya amince da kayen da ya sha tare da ɗaukar ƙaddara.
Duk da ba haka Sani Danja ya so ba, sai dai dama can ya bayyana cewa siyasarsa ba ta 'a mutu ko a yi rai' ba ce, ya fito ne domin ci gaban al'umma.
Abba El-Mustapha, shugaban hukumar tace fina finai da dab'i ta Kano, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Haka a ke son siyasa. Hon Sani Musa Danja ya taka kafa da kafa domin taya Hon Ogan Boye murnar samun nasarar dan takarar ciyaman na Nassarawa."
Mutane sun karfafi Sani Danja
Awanni bayan sanar da sakamakon, Sani Danja wallafa "Masha Allah" a shafinsa na Facebook wanda ya jawo martani daga masoyansa.
Wani Najib Danjuma Roni ya ce sam ba su yarda wannan tsari ba, yana mai cewa ba a fi Sani Danja wahaltawa jam'iyyar ba kuma ba a fi shi akidar Kwankwasiyya ba.
"Toh ni dai daga rana irin ta yau ba ni ba Kwankwasiyya wallahi, mai gida Danja Allah ya sa haka ya fi alkairi, ni daman domin kai na keyi wallahi."
- A cewar Najib Roni.
Yusuf Falaki ya bayyana ra'ayinsa da cewa:
"Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi. Insha Allah kai ne mai tallafawa gwamna na musamman kan matasa da wasanni."
Shamsiyya Abubakar ta bayyana cewa:
"Muna fatan alkairi. Allah shi ne shaida, kai muka so amma Allah ya yi na shi iko, don haka ka yi hakuri, Allah ya kawo rabo mai yawa mai albarka."
A zantawarmu da Abba Hassan daga jihar Kano, ya ce gaskiya bai ji abin da aka yiwa Sani Danja ba, amma a hannu daya kuma Ogan Boye ya fi jarumin cancanta.
"Na san cewa shi ma Sani Danja ya na da ta shi daukakar da kuma jama'a, amma idan ana maganar siyasa, to a barwa Ogan Boye, shi ne ya cancanci kujerar."
Maryam Isiyaku, wadda ita ma 'yar gwagwarmaya ce daga Nasarawa, ta ce ta so ace an tsayar da Sani Danja saboda kasancewarsa mutum na mutane.
Sai dai Maryam ta yi fargabar cewa yayin yadda mutane ke kallon Sani Danja a fina finai zai iya yin tasiri a kansu ranar zabe, wanda zai iya hana NNPP samun nasara.
Ali Jita ya fice daga NNPP
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin soyayya da siyasa, Ali Jita ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya inda ya koma gidan Sanata Barau Jibrin.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ne ya sanar da ficewa Ali Jita daga NNPP zuwa APC inda ya ce mawakin ya yi alkawarin taimakawa APC ta cimma gaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng