Shugaban Majalisa Ya Rantsar da Ragowar Mambobin APC bayan Watanni Suna Jira

Shugaban Majalisa Ya Rantsar da Ragowar Mambobin APC bayan Watanni Suna Jira

  • Daga ƙarshe shugaban majalisar dokokin Plataeu ya rantsar da ragowar ƴan majalisar na jam'iyyar APC mai adawa a jihar
  • Honarabul Gabriel Dewan ya rantsar da ƴan majalisar ne a ranar Larabawatanni bayan hukuncin babban kotun ɗaukaka ƙara
  • Da take martani kan lamarin, jam'iyyar APC ta caccaki shugaban majalisar bisa lokacin da ya ɓata kafin ya rantsar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Shugaban majalisar dokokin jihar Plateau, Honarabul Gabriel Dewan, ya rantsar da ragowar ƴan majalisar na jam'iyyar APC.

Shugaban majalisar ya rantsar da ragowar ƴan majalisar guda biyar ne bayan sun kwashe watanni suna jiran ya yi hakan.

An rantsar da 'yan majalisar APC a Plateau
Gabriel Dewan ya rantsar da ragowar 'yan majalisar APC a Plateau Hoto: Dewan Kudangbena Gabriel
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban majalisar ya rantsar da su ne a ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024.

Kara karanta wannan

2027: Kiran Kwankwaso, Atiku da Obi su tararwa Tinubu ya fusata jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rantsar da mambobin APC a Plateau

Jaridar The Nation ta ce mambobin da aka rantsar su ne Owen Dagogot (Qua’an-Pan ta Arewa), Theodore Maiyaki (Qua’an-Pan ta Kudu) da Yakubu Sanda (Pengana).

Ragowar su ne: Dachung Dadon (Riyom) da kuma Dalyop Gyang (Shendam ta Kudu).

Mambobin da aka rantsar na daga cikin ƴan majalisa 15 na APC da ɗaya na jam'iyyar LP da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasararsu a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

A ranar, 5 ga watan Afirilu, shugaban majalisar ya rantsar da guda tara daga cikinsu bayan sun sanya hannu kan takardar yin murabus.

Sai dai, sauran guda bakwai ɗin sun yi zargin cewa an ƙi rantsar da su ne saboda sun ƙi yarda su sanya hannu kan takardar yin murabus ɗin.

A makon da ya gabata ne aka rantsar da guda biyu daga cikinsu a lokuta daban-daban.

Kara karanta wannan

APC ta kwancewa Tinubu zani a kasuwa kan tsadar rayuwa

Me APC ta ce kan lamarin?

Muƙaddashin kakakin jam'iyyar APC na jihar Plateau, Shittu Bamaiyi, ya caccaki shugaban majalisar saboda lokacin da ya ɓata kafin ya rantsar da su.

Shittu Bamaiyi ya bayyana cewa shugaban majalisar ya hana mutanen mazaɓun da ƴan majalisar suka fito ƴancin samun wakilci har na tsawon wata takwas.

APC ta yi wa shugaban majalisa barazana

A wani labarin kuma, kun ji cewa jamiyyar APC a jihar Plateau ta yi barazanar zuwa kotu kan shugaban majalisar jihar saboda kin rantsar da mambobin majalisar.

Jam'iyyar APC ta ce za ta ɗauki mataki kan shugaban majalisar, Hon. Gabriel Dewan kan biris da rantsarwar da ƴan majalisu 16 a majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng