"Zaluncin Gwamnatin Tinubu Ya fi na Soja:" Atiku Ya Soki Yadda Ake Murkushe Kungiyoyi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu saboda matakin da ta dauka kan NLC
- Atiku Abubakar ya ce yadda gwamnatin kasar nan ke kokarin murkushe kungiyoyin kwadago na nuna tsagwaron zalunci
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma buga misali da yadda aka kama wani dan jarida, inda bayan an sake shi aka ce kuskure ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki yadda gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin murkushe kungiyoyi masu zaman kansu.
Ra'ayin Atiku Abubakar na zuwa ne bayan jami'an tsaron fararen kaya (DSS) sun cafke shugaban kungiyar kwadago da kutsawa ofishin SERAP.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya yi takaicin yadda ake kokarin murkushe muryar kwadago ta hanyar kama shugabanta, Joe Ajaero.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da zalunci
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da zalunci fiye da na lokacin mulkin sojoji a Najeriya.
Atiku ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kokarin dakile ayyukan kungiyar kare hakkin dan Adam da tattalin arziki (SERAP) ya saba doka kuma keta hakki ne.
Atiku ya shawarci gwamnatin Tinubu
Jagora a jam'iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin tarayya kan yadda ya kamata ta yi amfani da jami'an tsaro a kasar nan.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zabubbukan baya ya ce kamata ya yi gwamnatin Tinubu ta yi amfani da jami'an tsaro wajen maganin yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
"A daina takura wa jama'a," Atiku
A baya mun wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin tarayya ta daina matsawa wadanda su ka yi zanga-zanga. Atiku na ganin dacewa ya yi gwamnati ta tattara karfinta wajen yakar yan ta'adda ba mutanen da ke neman a inganta rayuwarsu ba ta hanyar fitowa tituna ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng