‘Babu Ruwanmu’ APC Ta Barranta daga Maganar Takarar Tinubu a 2027
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan zancen takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027
- Daraktan yada labaran jami'yyar APC na kasa ya bayyana matsayin jam'iyyar kan fara lika allunan takarar shugaban kasar
- A makon nan ne aka hango babban allon da yake tallan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 a birnin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Maganar takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027 ta cigaba da jan hankulan al'umma.
Hakan ya biyo bayan ganin wani allo dauke da hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zaben shekarar 2027 a Abuja.
Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktan yada labaran jami'yyar APC na kasa ya bayyana matsayinsu kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bullowar allon takarar Tinubu a 2027
Legit ta ruwaito cewa an hango wani babban allo da ke dauke da hoton shugaban kasa da ke ishara da shirin fara neman zaben shekarar 2027.
Hakan na zuwa ne bayan Bola Tinubu yana cikin shekara ta biyu da hawa mulkin Najeriya duk da cewa bai bayyana ko zai tsaya takara ba ko akasin haka.
Yan Najeriya na cigaba da kokawa kan yadda tsadar rayuwa ke kara jefa su a matsala sakamakon tsare tsaren Bola Tinubu.
2027: APC ta barranta da allon Tinubu
Daraktan yada labaran jami'yyar APC ya ce ba su da hannu wajen lika hoton shugaban kasa da nufin takara a zaɓen 2027 mai zuwa.
Yayin da yake nesanta APC daga allon, Daraktan ya ce yawanci ana samun wasu masoya da magoya baya na saka irin allunan a wurare.
Legit ta ruwaito cewa an tuntubi hadimin shugaban kasa kan harkokin sadarwa, Bayo Onanuga amma bai amsa wayar tarho ba.
An bukaci Tinubu ya rage kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa karin kudin man fetur a Najeriya na cikin abubuwan da suka cigaba da jan hankulan al'umma saboda wahala da aka shiga.
Kungiyoyi daban daban a Kudu da Arewacin Najeriya sun nuna takaici kan karin kudin man fetur da aka samu a Najeriya a makon da ya wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng