2027: Jam'iyyar Labour Ta Canja Shawara, Ta Fasa Ajiyewa Peter Obi Tikitin Takara

2027: Jam'iyyar Labour Ta Canja Shawara, Ta Fasa Ajiyewa Peter Obi Tikitin Takara

  • Da alama rikicin jam'iyyar Labour zai sake daukar sabon salo yayin da wani tsagin jam'iyyar ya ce ba zai ajiyewa Peter Obi tikitin takara ba
  • Tsagin jam'iyyar karkashin Julius Abure ya ce zai ba dukkanin 'yan Najeriya da suka cancanta damar neman tikitin takara a zaben 2027
  • Matakin da Abure ya dauka ya sabawa matakin da aka cimmawa a babban taron jam'iyyar wanda ya ayyana Obi a matsayin dan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam'iyyar Labour (LP) a karkashin Julius Abure ta ce za ta ba dukkanin 'yan Najeriya da suka cancanta damar tsayawa takara karkashinta a zaben 2027.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da jam'iyyar ta sanar da cewa za ta ajiyewa Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027 domin ya kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Jam'iyyar Labour ta yi magana kan wanda za ta ba tikitin takara a 2027
Jam'iyyar Labour ta fasa tanadarwa Peter Obi tikitin takara na zaben 2027. Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Jam'iyyar LP ta watsawa Obi kasa a ido

Tsagin Abure ya dauki matsayar fasa ajiyewa Peter Obi tikitin ne bayan da ya gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa a Abuja ranar Litinin, inji rahoton The Cable.

Wata sanarwar bayan taro daga jam'iyyar ta bayyana cewa:

"NEC a zamanta ta waiwayi hukuncin babban taron Labour na kasa wanda ya tanadin tikitin takarar shugaban kasa da na gwamna ga Peter Gregory Obi da Alex Otti.
"Saboda haka, muna sanar da cewa mun ba dukkanin 'yan Najeriya da suka cancanta damar neman tikitin jam'iyyar tun daga matakin kujerar shugaban kasa zuwa 'yan majalisu."

Labour ta gargadi Gwamna Otti

Tsagin Abure ya ce Alex Otti, gwamnan jihar Abia, ba shi da hurumin kiran taron masu ruwa da tsaki wanda ya samar da kwamitin riko karkashin jagorancin Sanata Nenadi Usman.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

"Gwamnan Abia, Alex Otti ba shi da ikon kiran taro a cikin kundin tsarin mulkin jam'iyya; sakatare na kasa ne kawai da amincewar shugaban kasa ke da iko.
“Gwamnan Abia ba shi da hurumin kiran taron 'yan majalisar zartarwar jam'iyyar na gundumarsa ba tare da amincewar shugaban gundumar ba."

- A cewar sanarwar.

Kalli bidiyon jawabin a nan kasa:

LP ta tsayar da dan takara

Tun da fari, mun ruwaito cewa jam'iyyar Labour (LP) ta ba da shawarin tanadar tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 ga Peter Obi.

Jam'iyyar Labour ta fara shawarwarin sake tsayar da Obi takara ne yayin da ta ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.