PDP Ta Fara Shirin Hukunta Tsohon Sanata Bayan Ya Kwance Mata Zani a Kasuwa

PDP Ta Fara Shirin Hukunta Tsohon Sanata Bayan Ya Kwance Mata Zani a Kasuwa

  • Kalaman da tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye ya fito ya yi kan shugabannin PDP ba su yi wa jam'iyyar daɗi ba
  • Shugabannin jam'iyyar na reshen jihar Kogi sun fara shirin dakatar da tsohon ɗan takarar gwamnan na PDP
  • Sun bayyana kalaman na Melaye a matsayin zallar munafurci domin ya amfana da abin da ya fito yana ƙorafi a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ta fara shirin dakatar da Sanata Dino Melaye.

Jam'iyyar ta buƙaci shugabanninta na ƙaramar hukumar Ijumu da su fara shirin dakatar da Dino Melaye biyo bayan sukar PDP da ya fito ya yi inda ya ce shugabanninta sun ruguza ta.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnati ta lissafa jami'o'in Benin, Togo da ta amince da su

PDP za ta hukunta Dino Melaye
PDP ta fara shirin hukunta Sanata Dino Melaye Hoto: Senator Dino Melaye
Asali: Facebook

Meyasa PDP za ta hukunta Dino Melaye?

Jam'iyyar PDP ta ce hakan ya zama wajibi ne domin dawo da ƙima da darajar shugabanninta, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ibrahim Dansofo, suka bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Lahadi a birnin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

"Tasirin Dino Melaye a siyasance ya kai matakin da ko kujerar Kansila ba zai iya samu ba."
"Sanata Dino Melaye ya zama cikon benci a jam'iyyar nan. Zarge-zargen da yake yi kan shugabannin PDP munafurci ne zalla."
"Shi kansa an ba shi tikitin takarar gwamna duk da sanin cewa ko zaɓen fidda gwani ba zai iya lashewa ba."

- Alhaji Ibrahim Dansofo

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ta ɗora alhakin halin da take ciki a yanzu kan Dino Melaye, inda ta yi iƙirarin cewa tikitin takarar da aka ba shi babban kuskure ne wanda ya jefa jam'iyyar cikin matsala.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya ga illar cire tallafin mai, ya tura sako ga Tinubu akan fetur

Jigon jam'iyyar PDP ya caccaki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Olabode George, ya yi magana kan ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar.

Bode George ya bayyana cewa akwai yiwuwar da Atiku Abubakar ya lashe zaɓen 2023, ba zai taɓuka wani abin kirki ba a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng