Dan Takarar PDP Ya Sha Kashi a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Bauchi
- Ɗan takarar jam'iyyar AAC a kujerar Kansilan mazaɓar Papa da ke ƙaramar hukumar Darazo a jihar Bauchi ya samu nasara
- Yunusa Muhammad ya lallasa abokin takararsa na jam'iyyar PDP mai mulki a jihar, Ashiru Mohamma Papa
- Ɗan takarar na AAC ya zo na ɗaya ne a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2024 bayan ya samu ƙuri'u 1,156
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Ɗan takarar jam'iyyar AAC ya kayar da takwaransa na jam'iyyar PDP a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Bauchi.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BSIEC), ta sanar da Yunusa Muhammad na jam'iyyar AAC a matsayin wanda ya lashe kujerar Kansila ta mazaɓar Papa a ƙaramar hukumar Darazo ta jihar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a yau Asabar, 17 ga watan Agustan 2024, aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan takarar AAC ya kada na PDP a Bauchi
Baturen zaɓe na ƙaramar hukumar Darazo, Muhammad Abdullahi ya sanar da sakamakon zaɓen bayan an kammala kaɗa ƙuri'a.
Da yake sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ke Darazo, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce ɗan takarar na AAC ya samu ƙuri'u 1,156 inda ya yi nasara kan abokin hamayyarsa na PDP Ashiru Mohammad Papa, wanda ya samu ƙuri'u 1,053.
Ɗan takarar jam'iyyar APC, Idris Mohammad ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 290.
"Ni Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayina na baturen zaɓen Kansila na mazaɓar Papa a jihar Bauchi wanda aka yi a ranar Asabar, 17 ga watan Agusta 2024, na tabbatar da Yunusa Muhammad na AAC bayan cika dukkanin ƙa'idojin da doka ta tanada a matsayin wanda ya lashe zaɓen."
- Muhammad Abdullahi Abubakar
PDP ta ƙwace ikon majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar Labour Party (LP) mai mulkin jihar Abia ta rasa ikon majalisar dokokin jihar Abia a hannun jam'iyyar PDP.
PDP ta yi nasarar ƙwace ikon majalisar dokokin jihar ne bayan rantsar da Aaron Uzordike a jiya Talata 13 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng