PDP Ta Yi Nasarar Kwace Ikon Majalisar Jiha, Jam'iyya Mai Mulki Ta Shiga Lahaula

PDP Ta Yi Nasarar Kwace Ikon Majalisar Jiha, Jam'iyya Mai Mulki Ta Shiga Lahaula

  • Jam'iyyar PDP ta yi nasarar kwace ikon Majalisar dokokin jihar Abia bayan samun karin wakilici kwanan nana
  • PDP ta samu karuwa da rantsar da Aaron Uzordike a yau Talata bayan umarnin kotu tun a watan Nuwambar 2023
  • Rantsar da Uzordike ya ba PDP damar samun mutane 12 yayin da LP take da 11 sai kuma jam'iyyar APC mai wakili guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Jam'iyyar LP mai mulkin jihar Abia ta shiga damuwa bayan kwace ikon Majalisa ta PDP ta yi.

PDP ta yi nasarar kwace ikon Majalisar jihar bayan rantsar da Aaron Uzordike a jiya Talata 13 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori korafin yan takarar APC da NNPP, ta fadi wanda ya lashe zaben Sanata

Jam'iyya mai mulki ta rasa ikon Majalisar jiha bayan PDP ta sha kanta
Jam'iyyar PDP ta kwace ikon Majalisar jihar Abia bayan rantsar da sabon mamba. Hoto: Legit.
Asali: Original

Jam'iyyar PDP ta kwace ikon Majalisar Abia

Uzordike ya shaidawa jaridar Leadership tsantsar jin dadinsa game da wannan nasara da kuma rantsar da shi da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan tabbatar da kujerarsa da kotu ta yi a zaben 2023 kan dan takarar LP, Destiny Nwagwu.

Kakakin Majalisar, Emmanuel Emeruwa ya ki bin umarnin kotun duk roko daga Uzordike da PDP da kuma masu ruwa da tsaki a jihar.

Yawan 'yan kowace jam'iyya a Majalisar Abia

Rantsar da Uzordike ya tabbatar da mambobin PDP a Majalisar 12 yayin da LP mai mulki ke da 11 sai kuma APC da wakili daya.

Jam'iyyar LP mai mulkin jihar ta samu har mutum 11 ne bayan sauya shekar wasu yan jam'iyyar YPP zuwa cikinta.

Uzordike ya bayyana jin dadinsa kan wannan nasara da ya samu inda ya yabawa Gwamna Alex Otti.

Kara karanta wannan

An nemi makiyaya 11 da shanu 33 an rasa a wata jihar Kudu, Miyetti Allah ta koka

Dan Majalisar ya godewa kakakin Majalisar da yan mazabarsa da suka tsaya tare da shi har zuwa wannan lokaci.

"Ina godewa jam'iyyata ta PDP da ta bani dama domin tsayawa takara karkashinta."

- Aaron Uzordike

Dan takarar shugaban kasa ya koma APC

Kun ji cewa Jam'iyyar APC ta yi babban kamu bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya watsar da jami'yyarsa.

Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu shi ya karbi tsohon dan takarar mai suna Dakta Cosmos Ndukwe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.