Majalisar Magabata: Buhari, Jonathan Sun Magantu kan Yadda Tinubu ke Mulkin Najeriya

Majalisar Magabata: Buhari, Jonathan Sun Magantu kan Yadda Tinubu ke Mulkin Najeriya

  • Tsofaffin shugabannin kasa, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun kada kuri'ar amincewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Shugaba Tinubu ya kira taron majalisar magabata ne a karon farko tun bayan da gwamnatinsa ta fara aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023
  • Buhari da Jonathan ne kawai tsofaffin shugabannin kasar da suka halarci taron da kansu; sauran sun halarta ne ta yanar gizo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar magabata da suka hada da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun kada kuri’ar gamsuwa da gwamnatin Bola Tinubu a ranar Talata 13 ga watan Agusta.

Majalisar ta bayyana gamsuwarta da yadda gwamnatin Tinubu ke gudanar da ayyukanta bayan ta saurari jawabin ministoci shida da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

'Yan majalisar magabata sun yi magana kan mulkin Shugaba Tinubu
'Yan majalisar magabata sun kada kuri'ar gamsuwa da mulkin Shugaba Tinubu. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da Bayo Onanuga, mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin yada labarai ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon ya ce:

"Majalisar magabata ta kada kuri'ar gamsuwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da majalisar ministocinsa, bayan sauraron jawabai daga ministoci shida da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu."

Mecece majalisar magabata ta kasa?

Majalisar magabata ta kasa wani bangaren gwamnati ne da ke ba da shawara ga tsarin mulki a Najeriya, wacce sashe na 153(1) na kundin tsarin mulkin 1999 ya kafa, inji shafin WikiPedia.

Majalisar ta kunshi shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa, da daukacin tsofaffin shugabannin kasa na farar hula da mulkin soja.

Sauran sun hada da dukkanin tsofaffin alkalan Najeriya (CJN), shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, da dukkanin gwamnonin jihohi.

Kara karanta wannan

Matasa miliyan 1 za su yi tattakin goyon bayan Tinubu bayan zanga zangar adawa

Babban aikin majalisar dai shi ne bai wa shugaban kasa shawara kan al'amuran da suka shafi kasa, musamman kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro da harkar siyasa.

Tinubu ya kira taron majalisar magabata

Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa a karon farko tun bayan hawansa mulki watanni 14 baya.

Wata majiya ta bayyana cewa majalsiar za ta yi magana ne kan wasu batutuwa 7, yayin da aka yiwa taron take da: "Alakar zanga-zanga da tsaron kasa da kuma yanayin tattalin arziki."

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.