“Wa’adinka Ya Kare”: Gwamna Ya Fusata Kan Ikirarin Mai Murabus a Gwamnatinsa

“Wa’adinka Ya Kare”: Gwamna Ya Fusata Kan Ikirarin Mai Murabus a Gwamnatinsa

  • Gwamnatin jihar Imo ta yi martani kan ikirarin tsohon shugaban hukumar kula da albarkatun mai, Mista Charles Oris
  • Gwamnatin ta karyata cewa Oris ya yi murabus daga mukaminsa inda ta ce daman can wa'adinsa ya kare tun a baya
  • Wannan na zuwa ne bayan ya sanar da ajiye mukaminsa da cewa zai fara shirye-shiryen neman takarar siyasa a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya caccaki Charles Orie kan ikirarin murabus daga gwamnatinsa.

Uzodinma ya karyata Oris inda ya ce wa'adinsa ne a kare a matsayin shugaban hukumar kula da arzikin man fetur na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya janye dokar hana Fita a Kaduna da Zaria, Ya Aikawa Malamai, Sarakuna Saƙo

Uzodinma ya dira kan wani da ya ce ya yi murabus a gwamnatinsa
Gwamna Hope Uzodinma ya karyata murabus din wani a gwamnatinsa. Hoto: Hope Ozodinma.
Asali: Facebook

Gwamna Uzodinma ya fusata game da Orie

Kwamishinan yada labarai, Declan Emelumba shi ya tabbatar da haka a cikin watan sanarwa, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Declan ya ce murabus din Orie bai inganta ba saboda wa'adinsa na kasancewa shugaban hukumar ya kare kafin nan.

Sanarwar ta ce duk da babu alaka mai tsami tsakanin gwamnan da Orie amma fayyace gaskiya ya zama dole, Daily Trust ta tattaro.

"A wannan yanayi, bai kamata ya yi murabus a mukamin da babu shi ba tun da wa'adin ya riga ya kare kuma babu tsawaitawa."

- Declan Emelumba

Imo: Murabus din Orie daga mukaminsa

Wannan na zuwa ne bayan Orie ya fitar da sanarwa zuwa ga Gwamna Uzodinma cewa ya yi murabus saboda dalilan siyasa.

Ya ce ya ajiye aikin ne saboda shirye-shiryen neman takarar siyasa a zaben 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke, mataimakin gwamna da majalisa ta tsige ya koma bakin aiki a ofis

"Bayan dogon nazari da addu'o'i, dole zan ajiye aikina saboda shirye-shiryen neman takarar siyasa a zaben 2027."
"Na yanke shawarar bayan nazari da kaina da iyalaina, ina mai tabbatar maka cewa na dauki matakin cikin girmamawa."

- Charles Orie

Zanga-zanga: Gwamnonin APC sun gargadi matasa

Kun ji cewa Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana damuwa kan yadda matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga a kasar.

Gwamnonin suka ce rashin ilimi ne musabbabin wannan zanga-zanga duk da sun sani an fada wani yanayi a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.