Zamfara: Dan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP? Gaskiya Ta Fito
- Yayin da ake yada jita-jitar cewa Hon. Aminu Jaji ya bar APC, jam'iyyar ta yi martani domin kore karairayin
- Tsagin jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta yi fatali da rade-radin inda ta ce babu wani shiri nan kusa na Jaji domin barinta
- Sakataren tsagin jam'iyyar, Mansur Khalifa ya tabbatar da haka inda ya bayyana irin gudunmawa da Jaji ya ke ba APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Tsagin jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta yi martani kan jita-jitar ficewar dan Majalisar Tarayya, Hon. Aminu Jaji daga APC.
Jam'iyyar ta yi fatali da rade-radin inda ta ce Jaji ba shi da wani shiri na barin jam'iyyar nan kusa.
APC ta ƙaryata zancen facewar Hon. Jaji
Sakataren tsagin jam'iyyar, Masur Khalifa Kaura shi ya tabbatar da haka a wata sanarwa a yau Asabar 11 ga watan Agustan 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kaura ya ce babu batun barin APC da Jaji zai yi saboda irin gudunmawar da ya ba jam'iyyar mai mulkin Najeriya.
Ya ce Jaji musamman ya ci wa Bola Tinubu karamar hukumarsa a zaben 2023 da ya wuce tare da tallata shi, Punch ta tattaro.
Zamfara: APC ta ja kunnen jama'a
"Mun samu labarin jita-jita daga wasu gurbatattu a jam'iyyar APC a Zamfara kan neman batawa Hon. Aminu Sani Jaji suna."
"Hoton da ake yaɗawa na Jaji da Rabiu Kwankwaso tsohon hoto ne tun lokacin kaddamar da Majalisa ta 10."
"Jaji ya kai ziyara ga Kwankwaso ne yayin da yake neman goyon bayan masu ruwa da tsaki a siyasa lokacin neman kujerar shugabancin Majalisar."
- Mansur Khalifa Kaura
Kungiya ta yi barazanar kiranye ga Hon. Jaji
A wani labarin, kun ji cewa wata a mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara sun fara shirin kiranye kan ɗan Majalisar Tarayya a yankin, Aminu Sani Jaji.
Jama'ar yankin suka ce sun yi nadamar zaben Hon. Jaji shiyasa suke kokarin daukar wannan mataki a kansa saboda rashin katabus.
Asali: Legit.ng