Bidiyo: Fusatattun Matasa Sun Lalata Manyan Allunan Hotunan Tinubu a Yobe
- Fusatattun matasan jihar Yobe sun lalata manyan allunan kan titi ɗauke da hotunan Tinubu, Shettima da Gwamna Buni
- An kafa allunan ne domin maraba da shugaban ƙasar zuwa ƙaddamar shirin karfafa noma da kiwo a jihar Yobe
- Sai dai, matasan sun ɗare kan allunan a wani bidiyo tare da fatattaka hotunan da ke ɗauke da sakon godiya da fatan sauka lafiya ga Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Damaturu, Yobe - Wasu fusatattun matasa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, sun lalata manyan allunan da aka kafa domin yi wa Shugaba Bola Tinubu maraba zuwa jihar.
A ranar Asabar, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Tinubu wurin ƙaddamar da wani shirin ƙarfafa noma a Yobe da aka yi a Damaturu.
"Muhimmancin noma a Najeriya" - Tinubu
A cewar Shugaba Tinubu, shirin babban abu ne a mulkinsa a ƙoƙarin inganta tsaron abinci, samar da ayyuka da faɗaɗa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar noma, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasar ya jaddada muhimmiyar rawar da noma yake takawa a cigaban ƙasa da tsaro, inda yace:
"Abinci shi ne ginshiƙin tsaro a kowacce al'umma. Shi ne ginshiƙin da ake gina lafiya a kai, walwala da daidaituwar tattalin arziki.
"Babu yadda za a yi mu cimma manufofinmu a matsayin gwamnati, a matakin jiha ko ƙasa, har sai da taimakon manomanmu."
Yobe: Matasa sun yago fastocin Tinubu
Sai dai, bayan kaddamar da shirin, an ga matasa a jihar a wani bidiyo da ya yaɗu suna hawa kan allunan dake ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu, mataimakinsa Shettima da Gwamna Mai Mala Buni.
"Mun gode Shugaban ƙasa. Allah ya kiyaye."
- Aka rubuta a jikin allon.
Fusatattun matasan sun lalata allunan tare da sauke hotunan dake ɗauke da sakon zuwa kasa.
Kalli bidiyon a kasa kamar yadda Nigeria Stories suka wallafa a X:
An garkame matashin mai kiran zanga-zanga
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa, matashin nan da yayi kira da a bankado malamai daga kan mumbari matukar suka hana zanga-zanga, mai suna Junaidu Abdullahi, yana gidan kurkuku.
Junaidu wanda aka fi sani da AbuSalma, yayi batan dabo bayan kwanaki da ya saki bidiyon bore ga malamai masu hana yin zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng