PDP Ta Fadi Lokacin Kwace Kujerun da Ta Rasa a Hannun Jam'iyyun Siyasa, Ta Sha Alwashi

PDP Ta Fadi Lokacin Kwace Kujerun da Ta Rasa a Hannun Jam'iyyun Siyasa, Ta Sha Alwashi

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta fara shirye-shiryen dawowa kan madafun iko a ƙasar nan ba da daɗewa ba
  • Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar sun gudanar da wani taro a jihar Enugu inda suƙa sha alwashin ƙwato muƙaman da jam'iyyar ta rasa a hannun jam'iyyun adawa
  • Gwamna Bala Mohammad ya nuna godiyarsa ga mai masaukin baƙi, Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu bisa irin tarbar da ya yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, ta sha alwashin ƙwato dukkanin muƙaman shugabancin da wasu jam’iyyun siyasa suke riƙe da su.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne ya yi wannan alƙawarin a wajen buɗe taron ƙungiyar da da aka yi ranar Laraba a Enugu.

Kara karanta wannan

Nade naden Tinubu: APC ta kwantar da hankalin Arewa, ta yi albishir ga masu jiran mukamai

PDP ta shirya dawowa kan mulki
Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP za ta kwato mukaman da ta rasa Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

A cewarsa taron na musamman ne a tarihin jam’iyyar domin sun je Enugu domin kafa tarihi da nuna jajircewarsu ga jam’iyyar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa taron ya ƙunshi gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka haɗa da kwamitin ayyuka na ƙasa da sassan jam’iyyar daban-daban, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Wane alwashi jam'iyyar PDP ta sha?

"A yau mun zo ne domin haɗa kanmu, mu tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyya da al’amura daban-daban a cikin mu."
"Maƙasudin zaman mu zai mayar da hankali kan shugabancin jam'iyya, tattauna batutuwan cikin gida na jam'iyya, babban taro da sauran abubuwan da muke buƙatar yi domin zama zaɓi mai kyau ga ƴan Najeriya."
"Lokaci ya yi da jam’iyyar za ta ƙwato matsayinta na shugabanci a dukkanin jihohin da wasu jam'iyyu ke iko da su."

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

- Gwamna Bala Mohammed

Gwamna Bala Mohammed ya yabawa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah bisa karɓar bakuncin taron da kuma kula da su tun lokacin da suka isa jihar a ranar Talata.

Karanta wasu labaran kan PDP

Sabon rikici ya kunno kai a PDP, kotu ta haramtawa jam'iyya gudanar da babban taro

PDP ta dauki mataki bayan kotu ta soke zaben fidda gwaninta na gwamna

'Yan majalisa sun ba gwamnan PDP sabon wa'adi kan kasafin kudin 2024

PDP ta dakatar da babban jigo

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar PDP ya dakatar da mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa a yankin Kudu maso Kudu.

Jam'iyyar ta ɗauki matakin ne kan Dan Orbih saboda zargin kawo tsaiko a gudanar da jam'iyyar a jihar Edo mai arziƙin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng