Takun Saƙar Wike da Fubara: Jigon PDP Ya Faɗi Hanyoyi 4 Na Magance Rikicin Rivers
- Takun sakar da ke tsakanin 'yan majalisa masu goyon bayan Nyesom Wike da Simi Fubara ya cigaba da kazanta a jihar Ribas
- Kwamared Usman Okai, jigon PDP, ya shawarci Nyesom Wike da Gwamna Fubara da su fifita ra'yin jihar Ribas kuma su sasanta
- A wata tattaunawa da Legit.ng, Okai ya lissafo shawarwarin da zasu hana rabewar kai da suka hada da bukatar Wike ya bar PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - Jigon jam'iyyar PDP, Usman Okai, yayi kira ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya da ya mayar da takobinsa a kube kuma yayi sasanci da wanda ya gajesa.
A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng a ranar Lahadi, Okai, 'dan takarar majalisar wakilai na Dekina/Bassa a zaben 2023, ya ce akwai bukatar Wike da Fubara su ajiye banbance-banbancensu a gefe.
A sakon baya-bayan nan zuwa ga Wike, Fubara ya jaddada cewa gara ya yi murabus da dai ya yi mulkin jihar Ribas a karkashin ikon ministan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da kotun daukaka kara ta yanke wani hukunci da ya janyo cece-kuce inda ta hana 'yan majalisa 25 masu goyon bayan Wike zaman majalisa.
Wike vs Fubara: Okai ya kawo shawara
Yayin da rikici ya yi kamari tsakanin 'yan majalisa masu goyon bayan Wike da Gwamna Fubara, Okai ya ce dole ne tsohon gwamnan jihar ya ci girma a lamarin.
Ya jero shawarwarin shawo kan matsalar kamar haka:
1. Sasanci ko barin jam'iyya
Da farko dai, tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike ya yi kokarin sasanci da Fubara tare da ajiye duk wasu banbanci domin cigaban Ribas da PDP.
Idan ya gagara yin hakan, ya duba yuwuwar barin jam'iyyar PDP ma damar ya fahimci ba zai iya aiki karkashin shugabancin Fubara ba.
2. Hadin kai da ladabtarwa
Abu na biyu shi ne, ya zama dole ga shugabannin jam'iyyar PDP da su dauki matakin hada kan jam'iyyar tare da tabbatar da cewa 'yan majalisar jihar sun yi aiki da gwamnan.
Kamar yadda jigon PDP ya ce, wannan rikicin na shafar jam'iyyar, da jama'ar jihar Ribas kuma dole ne sai da hadin kai ake samun cigaba.
3. Shawo kan matsala a shari'ance
Abu na uku, majalisar jihar da ke fama da rabuwar kai yanzu haka tana kotu, dole ne ta yi sasanci ta hanyar shari'a.
Dole ne dukkanin bangarorin su mutunta doka tare da baiwa tsarin shari'a damar yin abinda ya dace.
4. Fifita jihar Ribas
A karshe, dole ne dukkanin bangarorin da abin ya shafa su fifita walwala da cigaban jihar Ribas tare da saka ajiye duk wani muradi na kashin kai.
Jama'ar jihar Ribas sun cancanci zaman lafiya da cigaba, kuma lokaci yayi da za su same shi ba tare da wannan rikici ya shafi ayyukan more rayuwarsu ba.
Usman Okai ya kara da cewa, ta hanyar daukar wadannan matakan ne kawai za a iya shawo kan rikicin jihar Ribas kuma jihar za ta cigaba cikin zaman lafiya da arziki.
Inda aka kwana a rikicin Fubara da Wike
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya ya sanar da halin da ake ciki kan rikicinsa da Fubara.
Ministan ya ce ba ya inuwa daya da Gwamna Siminalayi Fubara kuma ba shi da hannu kan rikicin da ya mamaye majalisar dokokin jihar Rivers.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng