Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Zaben Gwamnan Kogi

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Zaben Gwamnan Kogi

  • Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kogi da jam'iyyar SDP da ɗan takararta suka shigar
  • Kotun mai alƙalai uku ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Usman Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan
  • Hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar na zuwa ne bayan ɗaukaka ƙarar da SDP da Muritala Ajaka suka yi kan tabbatar da nasarar Usman Ododo da kotun zaɓe ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Usman Ododo a matsayin gwamnan jihar Kogi.

A ranar Alhamis kotun mai alƙalai uku ta yanke hukuncin yin watsi da ƙarar jam’iyyar SDP da ɗan takararta na gwamna Murtala Ajaka suka shigar.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta shirya yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar d agwamnoni

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Usman Ododo
Kotun daukaka kara ta tabbatar da Usman Ododo a matsayin gwamnan Kogi Hoto: Ahmed Usman Ododo, Muritala Ajaka
Asali: Facebook

Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da buƙatar da masu ɗaukaka ƙarar suka gabatar a gabanta, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Ododo

Kotun ta ce sun gaza gabatar da sahihin hujjoji da za su tabbatar da zarge-zargen da suke yi na maguɗin zaɓe, aringizon ƙuri’u da kuma yin amfani da takardun bogi, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce kotun zaɓen gwamnan jihar Kogi ta yi daidai da ta yi watsi da hujjar da masu shigar da ƙarar suka gabatar saboda zama abubuwan jita-jita.

A cewar kotun, zargin Ododo ya ba hukumar INEC takardun jabu, lamari ne na kafin zaɓe wanda babbar kotun tarayya ta yi hukunci a kai ba kotun zaɓe ba.

Kotun ta ce hakan ya faru ne kafin gudanar da zaɓen gwamnan na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar, saboda haka kotun zaɓen ba za ta saurare shi ba.

Kara karanta wannan

PDP ta dauki mataki bayan kotu ta soke zaben fidda gwaninta na gwamna

Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jam'iyyar AC da ɗan takararta Olayinka Braimoh da jam'iyyar PRP da ɗan takararta, Dakta Abdullahi Bayawo suka shigar kan nasarar Ododo saboda rashin cancanta.

Gwamna Ododo ya tsawaita wa'adin ciyamomi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Majalisar jihar ta ƙara wa'adin shugabannin riƙon ne zuwa watanni shida domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng