Ana Murnar Samun ’Yancin Kananan Hukumomi, Ciyaman Ya Nada Hadimai 100
- Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Chijioke Ihunwo ya yi abin a yaba kan nadin mukamai
- Ihunwo ya nada akalla masu ba shi shawara na musamman guda 100 da za su taimaka masa a shugabancinsa
- Shugaban karamar hukumar ya bukaci sababbin masu mukaman da su tabbatar da yin aiki tukuru a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Shugaban karamar hukuma a jihar Rivers ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 100.
Chijioke Ihunwo da ke jagorantar karamar hukumar Obio-Akpor shi ya dauki matakin domin inganta shugabancinsa.
Shugaban karamar hukuma ya nada hadimai 100
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ihunwo ya fitar a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ihunwo ya bukaci sababbin wadanda aka nada mukamin da su tabbatar sun yi aiki domin ci gaba da bin tsarin Gwamna Siminalayi Fubara.
Ya taya su marnar samun wannan dama inda ya hore su da su yi aiki tukuru domin ganin an samu ci gaba da tsare-tsaren gwamnatin jihar, cewar Sahara Reporters.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da gwamnoni kan kananan hukumomi.
Wadanda suka samu mukaman a Rivers
Daga cikin wadanda aka nada mukaman sun hada da Clement Ifelen Nwaru da Augusta Dafugbo Jaja da Bariasa Juliet Doba da Chigozie Emmanuel Esinuelo da Stella Nkechi Worlu da kuma Ogbonna Ezinne Stella.
Sauran sun hada da Charity O. Amadi da Ejekwu Theresa Nkiruka da Ijeoma Wosu da Orlu Grace Oluchi da Emilia Seibidor da Silverline Oluchi da Blessing Worlu da Blessing Ndidi Chinda da kuma Wosu Elizabeth Obinuchi.
Fubara ya fadi amfanin hallaci a rayuwa
Awani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya bayyana abin da yasa ba ya daukar wasu matakai.
Fubara ya ce tuna halacci yake hana shi daukar wasu matakai masu tsauri duk da zarginsa da ake yi da butulci.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng