"Wannan Faɗa Za Ta Yi Garɗi": El Rufai Ya Shiga Sukar Uba Sani, Ƴan Najeriya Sun Yi Martani

"Wannan Faɗa Za Ta Yi Garɗi": El Rufai Ya Shiga Sukar Uba Sani, Ƴan Najeriya Sun Yi Martani

  • Yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Nasir El-Rufai da Uba Sani, rigimar ra dauki sabon salo a jihar Kaduna
  • Tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya taya sukar Uba Sani bayan caccakar gwamnatinsa da aka yi kan rashin katabus
  • El-Rufai ya yi martani kan wata wallafa da aka yi inda ƴan Najeriya da dama suka tofa albarkacin bakinsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi martani bayan caccakar gwamnatin Uba Sani.

El-Rufai ya yada wallafar da aka yi domin nuna damuwa kan halin da jihar Kaduna ta tsinci kanta.

El-Rufai ya yi martani bayan sukar gwamnatin Uba Sani
'Yan Najeriya sun yi martani bayan El-Rufai ya taya sukar gwamnatin Uba Sani. Hoto: @elrufai, @ubasanius.
Asali: Twitter

El-Rufai ya taya sukar gwamnatin Uba Sani

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

Tsohon gwamnan ya yi martanin ne bayan @IU_Wakili ya wallafa wasu hotuna da ke sukar gwamnatin Uba Sani a shafin X a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hotunan an nuno bola a wurare da dama wanda ke nuna gwamnatin jihar Kaduna ba ta aiki ko kadan a jihar.

"Sun dauka wasa muke yi da muka ce musu cikin watanni kadan Uba Sani ya sauya jihar Kaduna."
"Wannan shi ne sauyin da muke samu daga gwamnan da ya fi kowa bajinta a Najeriya."

- Imran Wakili

A martaninsa, El-Rufai ya rubuta cewa daga Allah muke kuma a gare shi za mu koma wanda ke nuna takaici kan halin da jihar ke ciki.

"Daga Allah muke, kuma a gare shi zamu koma."

- Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

El Rufai ya sake caccakar Uba Sani, ya fadi makarkashiyar da aka yi masa

Ƴan Najeriya da dama sun yi martani game da martanin El-Rufai bayan caccakar gwamnatin Uba Sani na jihar Kaduna.

Abdulaziz Na'ibi Abubakar:

"Ka yi maganinsa, da kuma Tinubu, mutan goyon bayanka."

FS Yusuf:

"Wanna jihar Kaduna ne da baka gyara ba, ka da ka nuna kai na kirki ne ka yi amfani da rashin katabus domin bata Uba Sani."

Stanley Ezinna:

"Ina son tambaya, mene ya saka El-Rufai amincewa da shi ya gaje shi a matsayin gwamna."

@von_Bismack:

"Wannan fada za ta yi suga, ba za mu bari ta wuce mu ba."

2027: Gwamnonin da ka iya samun matsala

Kun ji cewa wasu gwamnonin jihohin Najeriya suna daukar wasu matakai da ba su yiwa al'ummar jihohinsu dadi.

Masana harkokin siyasa sun lissafo gwamnonin da ake hasashen za su iya samun matsala a zaben 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.