Kaduna: Tsofaffin Kwamishinoni Sun Fadi Gaskiya Kan Zargin El Rufai Ya Wawure N423bn

Kaduna: Tsofaffin Kwamishinoni Sun Fadi Gaskiya Kan Zargin El Rufai Ya Wawure N423bn

  • Tsofaffin kwamishinoni takwas na Kaduna sun yi karin haske kan rahoton majalisar jihar da ya zargi tsohuwar gwamnati da almundahana
  • Tsofaffin mukarraban gwamnatin sun karyata rahoton majalisar da ya ce gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423
  • Hakazalika tsofaffin kwamishinonin sun ce akwai basussukan da gwamnatin El-Rufai ta nemo amma gwamnatin Uba Sani ce ta karbi kudin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsofaffin kwamishinonin Kaduna a zamanin Nasir El-Rufai sun ce har yanzu gwamnatin Uba Sani na cin moriyar basussukan da tsohuwar gwamnatin jihar ta nemo.

Tsofaffin mukarabban gwamnatin El-Rufai sun kuma yi magana kan rahoton majalisar jihar da ya nuna tsohon gwamnan ya karkatar da Naira biliyan 423.

Kara karanta wannan

El Rufai ya sake caccakar Uba Sani, ya fadi makarkashiyar da aka yi masa

Tsofaffin kwamishinonin Kaduna sun yi magana kan zambar N423bn
Tsofaffin kwamishinonin Kaduna sun kare Nasir El-Rufai daga zargin zambar N423bn. Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Zargin rashawa a kan gwamnatin El-Rufai

A zantawarsu da manema labarai a Abuja, a ranar Talata, tsofaffin kwamishinoni takwas daga gwamnatin ta El-Rufai sun karyata zarge-zargen majalisar Kaduna, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin jami’an sun yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnatin El-Rufai na cewa ita ce ta karbo dukkanin basussukan da suka yi wa jihar katutu a yanzukafin ta bar ofis a Mayun 2023.

Sun kuma bayyana zargin da majalisar dokokin Kaduna ta yi na cewa tsohuwar gwamnatin ta karkatar da kudaden jihar N423bn a matsayin rashin adalci.

Tsofaffin kwamishinonin da suka kare El-Rufai

Tsofaffin kwamishinonin da suka yi magana da manema labarai sun hada da Jafaru Sani (ma’aikatar muhalli da ilimi), Hafsat Baba (ma’aikatar jin dadi da bunkasa jama’a) da Thomas Gyang (ma'aikatar ayyuka, tsare-tsare da kasafin kudi).

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya fallasa gwamnati, an gano Uba Sani yana ‘karya’ da ayyukan El-Rufai

Sauran sun hada da: Bashir Saidu (ma’aikatar kudi); Ibrahim Husaini (ma’aikatar noma da muhalli), Aisha Dikko (ma’aikatar shari’a), Fausat Ibikunle (ma’aikatar gidaje da raya birane), da Idris Nyam (ma’aikatar kasuwanci, kirkira da fasaha).

Sun bayyana tuhumar da majalisar ta yi a matsayin kamfe na batanci ga tsohon gwamnan, inda suka bayyana cewa rahoton ya dogara ne da wasu alkaluma da aka gina su akan karya.

Gwamnatin El-Rufai ta karbo tulin bashi?

Jaridar The Punch ta ruwaito tsohon kwamishinan muhalli, Mista Sani, ya ce akwai kuskure a rahoton majalisar da ya nuna tsohuwar gwamnati ta karbo bashin makudan kudi.

"Akwai basussukan da har gwamnatin El-Rufai ta sauka daga mulki a Mayun 2023 ba a karbe su ba, sabanin abin da shafi na 112 zuwa 116 na rahoton majalisar ya nuna."

Mista Sani ya kuma ce akwai basussukan da gwamnatin El-Rufai ce ta nemo su, amma gwamnatin Uba Sani ce ta karbi kudin, kuma ta ke amfani da su.

Kara karanta wannan

Sanatocin kudu maso gabas sun gana da Ministan shari'a domin a saki Nnamdi Kanu

El-Rufai ya yi karar majalisar Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu kan tuhumarsa da ta yi da zambar N432bn a shekaru takwas na mulkinsa.

El-Rufai ya shigar da kara kan take 'yanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ya ke neman kotun ta wofantar da rahoton kwamitin majalisar na bincikar gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.