2027: Gwamnoni 5 da Ka Iya Rasa Damar Zarcewa Wa'adi Na 2 Saboda Wasu Dalilai
'Yan siyasar Najeriya da dama sun fara shirye-shiryen zaben 2027 inda kowa ke kokarin fadi-tashi domin ganin ya samu abin da ya ke nema.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Sai dai akwai wasu gwamnoni wadanda ke wa'adinsu na farko da ake ta hasashen za su iya samun matsala a neman wa'adinsu na biyu.
Wasu daga cikinsu da ke shekarunsu na farko madadin gina al'umma da siyasarsu domin zabe sun buge da shiga rigima ko da iyayen gidansu ko kuma sauya wasu tsare-tsare da ka iya jawo musu matsala.
Masu hasashe sun ce akwai wadanda suka taba masarautu wanda zai iya zama matsala a gare su musamman ta bangaren al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta jero muku wasu gwamnoni da ake hasashen za su iya samun matsala a neman zarcewa a zabe.
1. Abba Kabir - Kano
An yi hasashen Abba Kabir zai iya fusknatar matsala a zabe mai zuwa idan ba a shawo kan matsalar masaratu da ake ciki ba a jihar.
Duk da caccakar Abdullahi Ganduje da aka yi kan kirkirar masarautun a baya, an kuma zargi Abba da gyara barna da barna madadin samo wata hanya.
2. Uba Sani - Kaduna
Uba Sani yana wa'adinsa na farko a matsayin gwamna wanda takun-saka tsakaninsa da mai gidansa Nasir El-Rufai ake ganin zai iya jawo masa matsala.
Gwamna ya kafa kwamitin binciken El-Rufai da yake zargin ya yi badakalar makudan kudi har N432bn lokacin mulkinsa a jihar.
3. Ahmad Aliyu - Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu a 'yan kwanakin ya tube sarakuna 15 a jihar da kuma kokarin samar da dokar rage karfin ikon Sarkin Musulmi a jihar.
Ana hasashen wannan mataki zai iya tasiri wurin zaben gwamnan a 2027 duba da yadda ake kushe kokarin taba kimar Sultan da ya ke yi.
4. Siminalayi Fubara - Rivers
Gwamna Sim Fubara shi ma yana wa'adinsa na farko amma ya dauko yaki da mai gidansa Nyesom Wike watanni uku bayan hawa mulkin jihar.
Masu fashin bakin siyasa na zargin Shugaba Bola Tinubu na goyon bayan Fubara a boye shiyasa yake samun dama kan Wike.
Wasu na ganin hakan zai iya yin tasiri a zabensa na 2027 yayin da zai nemi takara domin zarcewa karo na biyu.
5. Alia Hyacinth - Benue
Gwamna Alia Hyacinth ka iya fuskantar barazana idan har bai yi sulhu da sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ba da ke rike da jam'iyyar a jihar.
Ana hasashen rigima da Akume da kuma bincikar tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom ka iya zama kalubale a gare shi a 2027.
Kasashen da suka amince da yarjejeniyar Samoa
Kun ji cewa kasashen Afirka da dama sun sanya hannu a yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce a kai musamman a Najeriya.
Tun bayan rahoton Daily Trust kan sanya hannu a yarjejeniyar, 'yan kasar da kuma malaman addini suke ta korafi a kai.
Asali: Legit.ng