Kano: Abba Ya Fara Samun Koma Baya, Shugabannin NNPP Sun Koma APC
- Shugabannin matasan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai adawa a jihar
- A jiya Litinin ne matasan suka bayyana sauya shekar yayin ganawa da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya
- Matasan sun bayyana dalilan da suka sanya su guduwa daga jam'iyyar NNPP duk da cewa ita ce mai rike da madafun iko a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugabannin jam'iyyar NNPP sun fara ficewa daga tafiyar Abba Kabir Yusuf a jihar Kano.
Hakan na zuwa ne bayan da wasu shugabannin matasa a karamar hukumar Kura suka sauya sheka zuwa jami'yyar APC.
Legit ta tatttaro labarin ne a cikin sakon da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ficewar matasa daga NNPP
Shugaban matasan jam'iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Kura, Idris Musa ya ce sun fice ne saboda jami'yyar ba ta dauke su a komai ba.
Idris Musa ya kara da cewa sun amince da yadda Sanata Barau Jibrin ke jagorantar al'umma saboda haka suka dawo jami'yyar APC domin mara masa baya.
Za a yi kokarin dawo da Kano APC
A lokacin da yake karɓarsu, Sanata Barau Jibrin ya tabbatar da cewa za su yi aiki tare wajen ganin jami'yyar APC ta karɓi jihar Kano daga hannun NNPP.
Sanata Barau ya ce akwai abubuwa da jiha ba za ta samu yadda ya kamata ba matuƙar gwamnan jihar ba ya jami'yya daya da shugaban kasa.
APC za ta hada kai a Kura
Haka zalika, Sanata Barau ya bayyana cewa ya yi umurni ga shugabannin jam'iyyar APC a karamar hukumar Kura da su rungumi wadanda suka sauya shekar.
Ya ce akwai bukatar hadin kai a tsakaninsu kamar yadda dama an san jami'yyar APC da kokarin yin hakan.
Ganduje zai yaki gaba a siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban APC na kasa, Ganduje ya bayyana kadan daga shirinsa na sanya siyasar kasar nan ta dauki saiti.
Abdullahi Umar Ganduje ya ce, zai hada kai da kowa don kawo karshen siyasar gaba a kasar nan muddin yana shugaban APC.
Asali: Legit.ng