“Yafi Yiwa Yankinsa Illa Kamar Buhari”: An Fadi Yadda Tinubu Ke Kassara Najeriya
- Tsohon darakta-janar na kungiyar gwamnoni, Salihu Lukman ya yi martani kan illar da Bola Tinubu ke yiwa Najeriya
- Lukman ya ce tsare-tsaren tattalin arziki na Tinubu suna kashe tattalin kasar madadin farfado da shi a kasar
- Ya ce illar kuma har ila yau, tafi yiwa yankinsa na Kudu maso Yamma fiye da sauran yankuna biyar na kasar da ake da su
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya yi magana kan tsare-tsaren Bola Tinubu.
Lukman ya ce matakan da Tinubu ke dauka sun fi yiwa yankinsa na Kudu maso Yammacin kasar illa fiye da ko ina.
Lukman ya fadi illar da Tinubu ke yi
Tsohon jigon APC ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lukman ya ce saboda tsare-tsarensa, mafi yawan kamfanoni da ke yankinsa sun fara barin Najeriya.
Ya ce mafi yawansu suna barin kasar ne saboda tafka asara da suke yi wanda yake zama illa ga 'yan kasar da suke aiki da su.
Tun bayan hawan Tinubu mulkin Najeriya, kamfanoni da dama sun bar kasar saboda tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatinsa.
Tinubu yana kashe yankinsa - Salihu Lukman
"Matsala ce yadda Tinubu yake gudanar da tattalin arzikin kasar wanda ke yi wa yankinsa illa kamar yadda Buhari ya kashe Arewa."
"Hatsarin da ke cikin faduwar naira da tashin farashin kaya zai fi yiwa yankin Kudu maso Yamma illa fiye da sauran yankuna."
"Yankin Kudu maso Yamma kusan tafi ko ina ci gaba a fannin tattalin arziki, barin kamfanoni Najeriya da matsalolin tattalin arziki zai fi yiwa yankin illa."
- Salihu Lukman
Salihu Lukman ya fice daga APC
A wani labarin mai kama da wannan, tsohon mataimakin shugaban APC a yankin Arewa maso Yamma ya fice daga jam'iyya mai mulki.
Salihu Lukman ya ce a yanzu ba shi da wani sauran amfani a jam'iyyar shi yasa ya yanke hukuncin watsar da kashinta domin tsira da mutunci.
Asali: Legit.ng