Jerin Gwamnoni 20 da Suka Ƙi Yarda a Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a Jihohinsu

Jerin Gwamnoni 20 da Suka Ƙi Yarda a Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a Jihohinsu

Akalla jihohi 21 a Najeriya ne ba su da zababbun shugabannin kananan hukumomi yayin da gwamnonin su suka ki gudanar da zaben amma suka kafa kwamitin riko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wannan na zuwa ne duk da kiraye-kiraye da ake yi na ganin an ba kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu, abin da ya kai ga Shugaba Bola Tinubu ya yi karar gwamnonin.

Jerin gwamnonin Najeriya da ba su yarda da zaben kananan hukumomi ba.
Sunayen jihohin da shugabannin riko ke tafiyar da harkokin kananan hukumomi. Hoto: @officialABAT, @NGFSecretariat
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa matakin da gwamnonin suka yi ya sabawa sashe na 7 na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya ce dole ne a zabi ciyamomi domin su gudanar da harkokin kananan hukumomi.

A halin yanzu Najeriya na da kananan hukumomi 774 a fadin kasar, kuma su ne ke aiki a matsayin matakin gwamnati na uku.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin kwamishinonin Legas da Tinubu ya ba manyan mukamai a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin jihohin da gwamnonin su suka ki yarda a gudanar da zaben kananan hukumomi.

1. Jigawa ta rusa zababbun ciyamomi

Gwamnatin jihar Jigawa ta rusa zababbun shugabannin kananan hukumomi 27 na jihar a ranar 28 ga watan Yuni, 2024.

Hakan ya biyo bayan gyaran dokar kananan hukumomi da majalisar dokokin jihar ta yi.

Dokar dai ta tsawaita lokacin gudanar da zaben ciyamomi da shekara guda tare da ba da umarnin nada kwamitocin riko kafin zaben.

2. Gwamna Fubara ya nada kwamitin riko

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya nada kwamitin rikon kwarya biyo bayan rigimarsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Wani tsagin majalisar dokokin jihar ya tsawaita wa’adin ciyamomi biyo bayan gazawar da gwamnan ya yi na gudanar da zaben kananan hukumomin jihar

Kara karanta wannan

Sabon mafi ƙarancin albashi: Gwamnoni 17 sun aikawa Tinubu muhimmiyar buƙata

3. Yaushe Anambra ta nada ciyamomi?

A ranar ranar 20 ga Yunin 2024, Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya nada shugabannin riko na kananan hukumomi 21. Ya yi hakan ta hannun majalisar jihar.

Majalisar ta tabbatar da nadin, inda ta bayar da misali da sashe na 20 na dokar kananan hukumomi na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, biyo bayan bukatar gwamnan.

4. Uzodimma bai taba yin zaben ciyamomi ba

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo bai taba gudanar da zaben kananan hukumomi ba tun da ya zama gwamna a 2020.

Zaben kananan hukumomi na karshe da aka gudanar a jihar shi ne na ranar 25 ga watan Agusta, 2018, wanda shi ne irinsa na farko cikin shekaru bakwai.

5. AbdulRasaq bai taba yin zaben ciyamomi ba

Kamar takwaransa na Imo, Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq bai taba yin zaben kananan hukumomi ba tun da ya zama gwamnan jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

An ruwaito cewa an gudanar da zaben kananan hukumomi na karshe a jihar a watan Nuwambar 2017, kuma kwamitocin riko ne ke tafiyar da harkokin kansilolin tun 2020.

Sauran gwamnonin da ke cikin wannan rukuni su ne:

6. Zamfara

7. Benue

8. Bauchi

9. Plateau

10. Abia

11. Enugu

12. Katsina

13. Kano

14. Ondo

15. Yobe

16. Osun

17. Delta

18. Akwai Ibom

19. Cross River

20. Sokoto

Ciyamomi 44 sun maka Abba a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugabannin kananan hukumomi 44 sun maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotun kan yunkurin gina gadojin Tal'udu da Ɗan'agundi.

An ce ciyamomin sun yi karar Gwamna Abba Yusuf ne saboda ya ce zai yi amfani da kudin kananan hukumomin domin gudanar da aikin gina gadojin a cikin kwaryar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel