Malamin Musulunci Ya Kunyata ’Yan Siyasa a Zaman Makokin Tsohon Gwamna

Malamin Musulunci Ya Kunyata ’Yan Siyasa a Zaman Makokin Tsohon Gwamna

  • Malamin Musulunci, Sheikh Muhydeen Bello ya caccaki 'yan siyasa kan yawan gaba da suke yi a tsakaninsu da juna
  • Malamin ya bayyana haka yayin bikin tunawa da marigayi tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi a birnin Ibadan a Oyo
  • Shehin malamin ya bayyana 'yan siyasar Najeriya a matsayin marasa tsoron Allah da son abin duniya duk da dukiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Malamin addinin Musulunci ya gargadi 'yan siyasa kan amfani da lokacinsu wurin aikata ayyukan alheri.

Malamin mai suna Sheikh Muhydeen Bello ya ce wata rana za su zamo abin Allah sarki bayan barin ofisoshinsu.

Malamin Musulunci ya caccaki 'yan siyasa a Oyo
Sheikh Muhydeen Bello ya shawarci 'yan siyasa kan son junansu. Hoto: Sheikh Muhydeen Bello Ajani.
Asali: Facebook

Sheikh Bello ya shawarci ƴan siyasa

Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin bikin tunawa da tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a Ibadan da ke jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce 'yan siyasar Najeriya ba su da godiyar Allah kan abin da ya hore musu inda ya ce mafi yawa ba su tsoron Allah a cewar The Guardian.

"Yan siyasa ba su bukatar dukiya, amma ba su taba godewa Allah da abin da suke da shi, ba ku da tsoron Allah, kuna tare da Ajimobi amma kun yake shi."
"Har yanzu wasu suna jin haushinsa duk da yana cikin kabari, kowa zai wuce kamar yadda Ajimobi ya bar duniya."
"Ba tare da hadin kai ba, ba za a iya ci gaba da ayyukan alheri na Ajimobi ba, yana da jama'a sosai da suka damu da shi."

- Muhydeen Bello

Malami ya koka kan halin ƴan siyasar

Malamin ya ce a matsayinsu na 'yan siyasa ya kamata su so junanku, Ajimobi ya rasu ya bar mutane a bayansa, ya kamata kowa ya bar abin da za a iya tunawa da shi a duniya.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Sheikh Bello ya bukace su da su kasance cikin zaman lumana da 'yan uwansu ba tare da gabar siyasa ba.

Malamin Musulunci ya magantu kan sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Adamu Dokoro ya magantu kan rigimar sarautar Kano.

Malamin ya ba Abba Kabir da Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero shawarwari kan gudanar da komai domin Allah a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.