Takaitaccen tarihin Sanata Abiola Ajimobi da ake rade-radin cutar COVID-19 ta kashe
A ranar 18 ga watan Yuni, 2020, aka fara yada labarin cewa Sanata Abiola Ajimobi ya cika. Hakan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya shafe makonni biyu ya na jinyar Coronavirus.
Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa Ajimobi ya na nan da ransa. Ga kadan daga cikin tarihinsa:
1. Haihuwa
An haifi Abiola Ajimobi ne a ranar 16 ga watan Disamba a shekarar 1949 a wani kauye da ake kira Oja-Iba. Mahaifinsa shi ne Ajimobi na kasar Ibadan, yayin da Kakansa kuma ya rike sarautar Sobaloju na kasar. Tarihi ya nuna ‘danuwan mahaifinsa ya rike Minista a gwamnatin Yamma a jamhuriya ta farko.
2. Karatu
Abiola Ajimobi ya yi karatun firamare ne a makarantar waliyyi Patrick da ke Oke-Padre da makarantar Ibadan Citu da ke Aperin duk a garin Ibadan, jihar Oyo.
Daga nan ya zarce makarantar sakandaren Lagelu Grammar School. Marigayin ya yi digiri ne a fannin tattalin kudi da kasuwanci a wata jami’a da ke garin Buffalo a birnin New York a kasar Amurka. Ajimobi ya yi digirgir a harkar kudi a wata jami’a a garin Illionois, Amurka.
KU KARANTA: Mai dakin Ajimobi ta warke, ta bar tsohon gwamna ya na jinya
3. Aure
A shekarar 1980, Ajimobi ya auri Sahibarsa Florence Ajimobi wanda ta haifa masa ‘ya ‘ya biyar. Daga cikin ‘ya ‘yansu akwai Idris Ajimobi wanda ke auren Fatima Ganduje.
4. Aiki
Bayan shekaru kusan 20, Ajimobi ya zama shugaban wani kamfani na National Oil wanda ke karkashin kamfanin man Shell a Najeriya. Bayan shekaru 26 ya na aiki da kamfanin, ya yi ritaya ya shiga siyasa.
5. Siyasa
Ajimobi ya gaji siyasa a gidansu inda ya fara jarraba farin jininsa a 2003, ya zama Sanatan Oyo ta Kudu a jam’iyyar AD. A 2007 a Ajimobi ya yi takarar gwamnan Oyo a ANPP amma ya sha kasa. A 2011 ya yi nasarar zama gwamna a ACN, ya kuma bar tarihi inda ya zarce a 2015. Ajimobi ya sauka daga kujerar gwamna a 2019, amma bai iya komawa majalisar dattawa ba.
6. Rashin lafiya
A farkon watan Yuni aka kwantar da Abiola Ajimobi a asibitin First Cardiology Consultants da ke Legas bayan ya kamu da cutar COVID-19. Daga baya aka sallami Mai dakinsa amma shi ya cigaba da jinya har yanzu da mu ke samun labari.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng