Sallah: "Ku Tuna da Wadanda ba su yi Layya ba" Malamin Musulunci ya Shawarci Musulmi

Sallah: "Ku Tuna da Wadanda ba su yi Layya ba" Malamin Musulunci ya Shawarci Musulmi

  • Wani malamin addinin musulunci, Dr Tajudeen Adebayo ya ba musulmin da za su yi yanka a sallar bana shawarar su tuna da wadanda Allah bai ba su ikon sayen abin yanka ba
  • Dr Tajudeen Adebayo ya bayar da shawarar ne yayin da matsin rayuwa ya hana wasu musulmin Najeriya sayen dabbar layya duk da saura kwanaki biyu bababr sallah
  • Malamin addinin ya shawarci wadanda ke fuskantar matsin rayuwa da ka da su tsunduma cikin bakin ciki, domin gaba ta fi baya yawa kuma ana sa ran a samu sauyi a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos- Duba da halin matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta ga kuma sallah babba na tunkarowa, wani malamin addinin musulunci, Dr Tajudeen Adebayo ya shawarci musulmi kan abin da ya kamata su yi.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

Dr Tajudeen Adebayo ya ce duk musulmin da ba shi da yadda zai yi domin yanka kamar yadda addini ya umarci mai hali ya yi, ka da ya shiga damuwa sosai.

Ragon sallah
Malamin addinin musulunci ya shawarci wadanda za su yi yanka su tuna da wadanda ba su yi ba Hoto: Jaouad k
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa malamin ya bayar da shawarar ne a jihar Legas, inda ya ce duk wanda ke fama da rashin abin hannu ya dage da addu’a amma ka da ya bari bakin ciki ya lullube shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ayi rabon abin yanka,” Dr. Adebayo

Malamin addinin Islama, Dr Tajudeen Adebayo ya shawarci musulmin da Allah SWT ya hore masu abin yanka da su taimakawa na kusa da su da ba su samu ikon yi ba da bikin sallah babba.

Ya bayar da wannan shawara ne ganin yadda ‘yan Najeriya su ke fama da kuncin rayuwa, yayin da kayan amfanin yau da gobe, ciki har da ragunan sallah su ka yi tashin gwauron zabo,.

Kara karanta wannan

Miliyoyin musulmi za su fara hajji, harin Isra'ila ya hana mutanen Gaza zuwa Saudiyya

” Idan matsin tattalin arziki bai baka damar yin yanka da sallar nan ba, ka da ka shiga damuwa da yawa. Akwai wata lokaci mai kyau a gaba.”
”Duk wada ya yi yanka ya raba ga wadanda ba su samu damar yi ba.”

Malamin ya tunatar da musulmi cewa jini ko naman dabbar da su ka yanka ba zai kai ga Allah SWT ba, sai dai niyyar da aka yi yankan da ita, kamar yadda Daily Post ta wallafa.

An cafke barayin ragunan sallah

A baya mun kawo muku labarin cewa asirin wasu barayin raguna ya tonu a babban birnin tarayya Abuja lokacin da su ke kokarin sayar da wasu ragunan sallah biyu da su ka sato a gidan wani bawan Allah.

An kama barayin kasa da awanni 48 bayan samun nasarar cafke wasu da ake zargi da satar shanu a kasuwar dabbobi ta Abaja a Abuja da niyyar cefanar da su ga masu sayen dabbar layya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.