Ana Nemansa Ruwa a Jallo: Gwamnan PDP Ya Ba Tsohon Ciyaman da Mutum 131 Mukami

Ana Nemansa Ruwa a Jallo: Gwamnan PDP Ya Ba Tsohon Ciyaman da Mutum 131 Mukami

  • Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya ba da mukami ga wani tsohon ciyaman da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa kisan kai
  • Wanda ake zargin na cikin mutane 132 da gwamnan ya nada mukamin masu taimaka masa da masu ba shi shawara na musamman
  • Iyalan tsohon dan majalisar dokokin jihar da aka kashe sun nemi Gwamna Kefas da ya janye nadin da ya yiwa wanda ake zargi da kisan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya ba da mukami ga wani tsohon shugaban karamar hukuma, wanda ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Kotu ta soke nadin da aka yiwa Sanusi II? Ga karin haske kan hukuncin

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa tana neman tsohon shugaban karamar hukumar ruwa a jallo bisa zargin kashe wani tsohon dan majalisar dokokin jihar.

Gwamnan Taraba ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa
Taraba: Gwamna ya nada tsohon shugaban karamar hukuma mukami da wasu mutum 131. Hoto:@GovAgbuKefas
Asali: Twitter

Gwamnan Taraba ya nada mataimaka 132

Gwamnan ya nada wanda ake zargin tare da wasu mutum 132 a matsayin masu ba shi shawara na musamman a ranar Laraba kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Barista Gibon Kataps ya fitar ta bayyana cewa:

"Gwamna ya amince da nadin sababbin manyan masu taimaka masa da masu ba shi shawara na musamman da ƙananan hadimai kan al'umma da ma'aikatun gwamnatin jihar Taraba."

Da dama dai na zargin gwamnan da bai wa masu kisan kai mafaka a cikin gwamnatinsa da kuma taimaka musu wajen kaucewa doka.

An fusata da nadin tsohon ciyaman

Jaridar The Sun ta ruwaito nadin ciyaman din da ake zargi ya tsere ya haifar da fushi a tsakanin iyalan wanda aka kashe, inda suka nuna kaduwa da matakin da gwamnan ya dauka.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Wani dan uwan marigayin da ya nemi a boye sunasa saboda yanayin tsaro ya bukaci gwamnan da ya janye nadin da ya yiwa tsohon shugaban karamar hukumar.

A cewar shi, hakan ne zai sa wanda ake zargin ya fuskanci shari’a a gaban kotu kamar yadda babban alkalin jihar, Mai shari’a Joel Agya, ya bayar da shawarar a babbar kotun jihar.

Sojoji sun kama masu garkuwa a Taraba

A wani labarin daga jihar Taraba, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin sun addabi yankin da ayyukan garkuwa da mutane.

Wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun mallaki bindigogi kirar AK-47 kuma sansaninsu yana Gadawa a kauyen Zunguri da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel