Rikicin PDP Ya Dau Zafi Yayin da Aka Kori Tsohon Dan Majalisa Ana Dab da Zaben Gwamna

Rikicin PDP Ya Dau Zafi Yayin da Aka Kori Tsohon Dan Majalisa Ana Dab da Zaben Gwamna

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Edo da ke yankin Kudu maso Kudu ta kori ɗaya daga cikin jiga-jiganta a jihar bayan ta zarge shi da cin dunduniyar jam'iyyar
  • Jam'iyyar ta kori Honorabul Omorogbe Ogbeide-Ihama wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne da ya wakilci mazaɓar tarayya ta Oredo a jihar
  • Korar Omorogbe daga PDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar wanda za a yi nan da ƴan watanni masu zuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Oredo a jihar Edo ta ce ta kori Honorabul Omorogbe Ogbeide-Ihama daga jam’iyyar.

Ogbeide-Ihama tare da Philip Shaibu, tsohon mataimakin gwamnan jihar, a makon da ya gabata sun bayar da gudummawar sakatariyar yaƙin neman zaɓensu na gwamna ga jam’iyyar APC reshen jihar.

Kara karanta wannan

An shirin zaben gwamna, jigon PDP ya yi maƙarƙashiya, jam'iyya ta kore shi

Jam'iyyar PDP ta kori jigonta a Edo
PDP ta kori tsohon dan majalisar wakilai a jihar Edo Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

An kori tsohon ɗan majalisar wanda ya wakilci mazaɓar tarayya ta Oredo a majalisar wakilai bisa zarginsa da cin dunduniyar jam'iyyar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓa ta 2, Lawrence Aguebor, ya bayyana korarsa daga jam’iyyar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Meyasa PDP ta kori Omorogbe Ogeide-Ihama?

Ya ce an ɗauki matakin korar tsohon ɗan majalisar ne a wani gagarumin taro da mambobi da shugabannin jam'iyyar na mazaɓar suka yi.

A cewarsa, tun da farko an dakatar da shi na tsawon kwanaki 30 bayan haka kuma aka kafa kwamitin ladabtarwa.

Ya bayyana cewa kwamitin ya rubuta masa wasiku kuma ya kira shi a waya ya zo a zauna har sau biyar, amma Ogbeide Ihama Omoregie ya kasa bayyana a gabansu.

Lawrence Aguebor ya kuma buƙaci jama'a da kada su ƙara wata hulɗa wacce ta shafi jam'iyyar PDP da Omorogbe Ogeide-Ihama.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: Kwankwaso ya bayyana masu son kawo hargitsi a Kano

Ƙanin gwamna ya fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jami'yyar PDP a jihar Edo, Benjamin Obaseki wanda ya kasance ƙanin gwamnan jihar ne ya fice daga jam'iyyar ana dab da zaɓen gwamna.

Benjamin wanda ƙanin Gwamna Godwin Obaseki ne ya yi ƙaurin suna a jam'iyyar inda ya kasance jigo kuma mai faɗa a ji a ƙaramar hukumar Oredo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel