"Kwankwaso Zai Yi Maka Illa": Buba Galadima Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Shiga Siyasar Kano

"Kwankwaso Zai Yi Maka Illa": Buba Galadima Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Shiga Siyasar Kano

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, jigon NNPP, Buba Galadima ya gargadi Shugaba Bola Tinubu
  • Galadima ya ja kunnen Tinubu da ya yi hankali da shiga lamarin siyasar Kano ko ya lalata siyasarsa a Najeriya
  • Jigon NNPP ya ce tun farko bai kamata Gwamnatin Tarayya ta nuna goyon bayanta ga bangare guda daya ba a rigimar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan shiga rigimar Kano.

Galadima ya ja hankalin Tinubu kan takalar Rabiu Kwankwaso saboda zai iya jawowa kansa matsala a siyasa.

Buba Galadima ya gargadi Tinubu kan lamarin siyasar Kano
Buba Galadima ya ba Bola Tinubu shawara kan shiga rigimar siyasar Kano. Hoto: @Kyusufabba, @officialABAT.
Asali: Twitter

Kano: Galadima ya ja kunnen Tinubu

Kara karanta wannan

Bayan APC ta buƙaci cafke shi, Kwankwaso ya tura sako ga tsohon gwamna

Jigon NNPP ya bayyana haka a faifan bidiyon YouTube yayin hira da Arise TV a jiya Talata 18 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata Tinubu ya yi hankali da shiga siyasar Kano ko kuma ya lalata damarsa ta shugabancin Najeriya a jihar.

"Gwamnatin Tarayya da Bola Tinubu su yi taka tsan-tsan da siyasar Kano ko kuma ya ruguza siyasarsa."

- Buba Galadima

Galadima ya koka kan bangarancin Tinubu

Jigon siyasar NNPP ya caccaki Gwamnatin Tarayya kan nuna goyon baya ga bangare daya inda ya ce bai kamata ta shiga lamarin sarauta ba.

Galadima ya yabawa ƴan jihar Kano kan yadda suka doge kan gaskiya duk da dambarwar sarautar jihar da ake ciki.

Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Tinubu da jam'iyyar APC da neman kawo rudani a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Kwankwaso ya ce suna neman rigima domin samun damar sanya dokar ta ɓaci a jihar saboda kwace mulkin NNPP.

Tinubu ya musanta zargin Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Sanata Rabiu Kwankwaso na cewa Shugaba Bola Tinubu na neman kawo rudani a jihar Kano.

Tinubu ya ce labarin babu kamshin gaskiya a cikinsa kuma an yi ne domin ba ta musu suna kawai.

Kwankwaso ya zargi shugaban da shirin sanya dokar ta ɓaci domin samun damar kwace mulkin NNPP daga hannunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.