Kwankwaso Ya Bankaɗo Abin da Ya Faru a 2019, Ya Tona Masu Rura Wutar Rikicin Sarauta

Kwankwaso Ya Bankaɗo Abin da Ya Faru a 2019, Ya Tona Masu Rura Wutar Rikicin Sarauta

  • Jagoran NNPP na ƙasa ya bayyana yadda ƴan Kwankwasiyya suka sha fama da maƙiyan siyasa tun zaɓen 2019 har zuwa yanzu
  • Rabiu Kwankwaso ya ce ga dukkan alamu waɗannan maƙiyan sun sake dawowa su wargaza Kano a rikicin sarautar da ke faruwa
  • Har yanzu ana ta taƙaddama kan sarautar Kano tun bayan lokacin da Gwamma Abba Kabir Yusuf ya dawo da Muhammadu Sanusi II a watan Mayu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa ya ce talakan jihar Kano ba ya ƙaunar zalunci da rashin adalci.

Tsohon gwamnna ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake jawabi ga dandazon ƴan Kwankwasiyya a wurin shagalin bikin Babbar Sallah da aka shirya a ƙofar gidansa.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP tayi martani, ta ce APC na yunƙurin ƙwace mulki daga Gwamna Abba

Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya Bayyana yadɗa suke fama da makiya tun zaben 2019 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya ce ƴan Kwankwasiyya mutane ne masu son zaman lafiya amma a koda yaushe suna fama da maƙiyan siyasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka zalunci Kwankwasiyya tun 2019

"A 2019 mun ci zaɓen gwamna amma makiyan Kano suka ƙwace ta hanyar amfani da hukumar zaɓe INEC da kotu da sauransu, yanzu ya zama tarihi.
"Haka a 2023 mun lashe zaɓe makiya suka yi ƙoƙarin kwacewa amma Allah ya nuna ikonsa, ya tabbatar da gaskiya da adalci."
"Amma ga dukkan alamu maƙiya sun kara dawowa duba da abubuwan da ke faruwa game da batun masarautar Kano."

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda mutane ke ƙara tururuwar shiga tafiyar Kwankwasiyya saboda ba su ƙaunar zalunci, rahoton The Nation.

"Maimakon haka jama'ar mu suka ƙara ƙarfi da aiki tukuru don jawo mutane zuwa cikin tafiyarmu, kuma ban yi mamaki ba saboda talakan Kano ba ya son zalunci."

Kara karanta wannan

An miƙa wa Bola Tinubu sunan wanda ya kamata ya naɗa a matsayin ministan jin ƙai

- Rabiu Kwankwaso

Asalin rikicin sarautar Kano

Idan ba ku manta ba Muhammadu Sanusi II ya zama Sarkin Kano na 14 a lokacin mulkin Rabiu Kwankwaso a 2014 bayan rasuwar marigayi Sarki Ado Bayero.

Amma magajin Kwankwaso, Abdullahi Ganduje ya tsige Sanusi II daga sarauta kuma ya kore shi daga Kano a shekarar 2020.

Aminu Bayero dan marigayi Sarki Ado Bayero ya gaji Sarki Sanusi a kan karagar mulki, inda gwamnatin Ganduje ta raba masarautar Kano zuwa gida biyar.

A watan Mayu, 2024 majalisar dokokin Kano ta soke dokar da aka yi amfani da ita wajen tsige Sanusi, sannan Gwamna Kabir Yusuf ya mayar da shi a matsayin Sarki na 16.

Kwankwaso ya caccaki Gwamnatin Tinubu

A wani rahoton na daban Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya na koƙarin tayar da yamutsi a jihar Kano domim cimma wata manufa.

Jagoran Kwankwasiyya ya bayyana yaƙinin cewa mutanen Kano ba za su bari wani ya wargaza masu zaman lafiya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262