"Jam'iyyar APC Ta Shirya Ƙwace Kujerar Gwamnan PDP a 2024," Sanata Ya Magantu
- Tsohon gwamnan Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya ce APC ta kammala shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamna a watan Satumba, 2024
- Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce jam'iyyar ta kudiri aniyar ƙwace kujerar gwamna daga hannun jam'iyyar PDP
- Darakta Janar na kwamitin kamfen APC ya buƙaci dukkan mambobin jam'iyyar su haɗa kai su yi aiki tare domin samun nasara a zaɓe mai zuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta shirya kwace kujerar gwamnan jihar a zaɓen da ke tafe.
Sanata Oshiomhole ya faɗi haka ne ranar Jumu'a a wurin kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC.
Kamar yadda Channels tv ta tattaro, hukumar zaɓe INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamna a jihar Edo ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taya APC zata lashe zaɓen Edo?
Da yake jawabi a taron, Oshiomhole wanda kuma tsohon gwamnan Edo ne, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta kuduri aniyar lashe zaben ta hanyar dimokradiyya.
“Muna so mu ci zabe ta hanyar dimokradiyya, ba mago mago, ba wuru-wuru, babu maguɗi ko tashin hankali.
"Muna fafutukar ganin mun sauya gwamnati cikin lumana, abin da dimokuradiyya ke nufi kenan,” in ji shi.
Shugaban kamfe ya nemi haɗin kai
A nasa jawabin, Darakta Janar na tawagar yakin neman zaben, Sanata Matthew Uroghide ya jaddada cewa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar suna da muhimmanci.
Ya buƙaci mambobin APC da su sa a ransu suna kan manufa ɗaya ne da suke son cimma wa ko da kuwa babu sunayensu a cikin tawagar yaƙin neman zaɓe.
Ya kuma tabbatar da cewa ƙofarsa a buɗe take na ya zauna ya saurari koke ko tambayoyi daga kowane mamba dangane da kamfen da za a fara gadan-gadan.
A rahoton Vanguard, Daraktan Kamfen ya ce:
"Don Allah mu yi aiki tare, ya zama dole mu yi aiki tare. idan akwai wata matsala ta jam'iyya ko kamfe ku zo ku same ni, kowa yana da muhimmanci."
APC ta samu ƙarin goyon baya
A wani rahoton na daban mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige, Philip Shaibu da tsohon ɗan majalisar tarayya sun koma bayan jam'iyyar APC.
Manyan jiga-jigan biyu sun bayar da gudummuwa mai tsoka ga kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar APC, Monday Okpebolo.
Asali: Legit.ng