Ganduje da APC Sun Samu Matsala Bayan Babban Jigo Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar

Ganduje da APC Sun Samu Matsala Bayan Babban Jigo Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC a jihar Edo ta yi rashin babban jigonta bayan ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar
  • Cif Francis Inegbeneki wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a mazaɓar Sanatan Edo ta Tsakiya ya raba gari da jam'iyyar
  • Ya bayyana cewa bai gamsu da yadda jam'iyyar take gudanar da abubuwa a karamar hukumarsa wanda hakan ya sanya shi ɗaukar matakin yin murabus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Jam'iyyar APC a jihar Edo ta samu koma baya bayan babban jigo a jam'iyyar ya yi murabus yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar.

Cif Francis Inegbeneki mataimakin shugaban jam'iyyar na mazaɓar Sanatan Edo ta Tsakiya, ya yi murabus daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa ya ɓarke a jam'iyyar Kwankwaso, NNPP ta dakatar da ɗan takarar gwamna

Jigon APC ya yi murabus a jihar Edo
Jigo a jam'iyyar APC a Edo ya yi murabus Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Cif Francis Inegbeneki ya sanar da murabus ɗin nasa ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Yuni da ya aikawa shugaban jam'iyyar na mazaɓa ta 9 a ƙaramar hukumar Esan ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ya yi murabus daga APC?

Ya bayyana cewa wasu abubuwa da suke faruwa a jam'iyyar a ƙaramar hukumarsa sun ci karo da yanayin tsarinsa na siyasa.

Yayin da yake bayyana cewa ya kamata jam'iyyar ta yi gyara a jihar, ya bayyana cewa murabus ɗinsa daga jam'iyyar APC ya yi ne domin ci gaban jam'iyyar a mazaɓar Sanatan Edo ta Tsakiya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Bayan shekara 25 a cikin siyasar jihar Edo kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC a jihar Edo, na yi amanna cewa na ba da gudunmawata wajen ci gaban jam'iyyar a mazaɓata, jiha da ƙasarmu Najeriya."

Kara karanta wannan

Komai nisan jifa: Matashi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan shekaru da damfara

"Sai dai, wasu abubuwa na faruwa a jam'iyyar a ƙaramar hukumata da jihar waɗanda suka ci karo da tsare-tsare na."
"Hakan ya sanya na sake yi duba kan makomar siyasa ta a jihar Edo tare da yanke shawarar abin da ya kamata na yi."
"Bayan kammala shawarwari da iyalaina, abokai da abokanan siyasa, ina so na sanar maka da cewa na yi murabus daga jam'iyyar APC da muƙamina na mataimakin shugaba."
"Wannan mataki ne mai wahala amma wanda ya kamata saboda ci gaban mutanen mazaɓata ta Sanata."

- Cif Francis Inegbeneki

Batun tsige Ganduje a APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar fara sauraron ƙarar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC.

Kotun ta sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar wacce ke neman a tsige tsohon gwamnan na jihar Kano daga shugabancin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel