"Babu Wanda Ya San El Rufai": Shehu Sani Kan Gwagwarmayar 'June 12', Ya Yabi Uba Sani

"Babu Wanda Ya San El Rufai": Shehu Sani Kan Gwagwarmayar 'June 12', Ya Yabi Uba Sani

  • Shehu Sani ya barranta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da shiga gwagwarmayar "June 12" a Najeriya
  • Shehu Sani ya bayyana haka yayin da ya ke karin haske kan juya maganarsa da aka yi a taron liyafa a birnin Tarayya Abuja
  • Sanatan ya ce lokacin da suke gwagwarmaya babu wanda ya san Malam Nasir El-Rufai amma Uba Sani ya taimake su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya magantu kan rawar Nasir El-Rufai a gwagwarmayar"June 12".

Shehu Sani ya ce babu wanda ya san Nasir El-Rufai a lokacin da ake cikin gwagwarmayar dawo da dimukradiyya.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya fallasa wanda ya jawo ake binciken gwamnatin El-Rufai

Shehu Sani ya yabawa Uba Sani yayin da ya bude El-Rufai
Shehu Sani ya yi karin haske kan juya maganarsa game da Nasir El-Rufai a gwagwarmayar "June 12". Hoto: Nasir El-Rufai, Shehu Sani, Senator Uba Sani.
Asali: Facebook

June 12: Shehu Sani ya tabo El-Rufai

Sanatan ya bayyana haka ne a shafin X yayin da yake karin haske kan rashin fahimtar maganarsa da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin kalamansa yayin liyafar cin abinci a ranar dimukradiyya, Sanatan ya yabawa Gwamna Uba Sani kan kokarinsa a gwagwarmayar.

Sai dai wasu sun juya masa magana inda suka alakanta maganar da Nasir El-Rufai madadin Uba Sani.

Shehu Sani ya magantu kan June 12

"Ina son gyara kuskuren da wasu gidajen jaridu suka yi kan wadanda suka tsaya mana a gwagwarmayar "June 12" ina magana ne kan gwamnan Kaduna, Uba Sani ba tsohon gwamna ba."
"Uba Sani ya kasance da mu da iyalanmu tsawon wannan lokaci a gwagwarmayar da muka yi har zuwa Arewacin Najeriya."
"Ya kasance tare da mu har lokacin da DSS suka kama shi, sannan ƴan sanda suka cafke shi tare da yi masa duka."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana ranakun hutun Babbar Sallah a Najeriya

"Falana da Mike Ozekhome da Femi Aborishade da Kanal Umar da Mrs Obe da Mrs Odumakin da John Danfulani da Kalat Ali da Nike Kuti da kuma Agbakoba za su shaida haka, amma ba a san El-Rufai ba lokacin gwagwarmayar."

- Shehu Sani

Shehu Sani ya fadawa Tinubu gaskiya

Kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa taken Najeriya ko kundin tsarin mulki ba zai taba hada kan ƴan ƙasar ba.

Sanatan ya bayyana haka ga Bola Tinubu inda ya ce adalci da daidaito shi ne kadai hanyar hadin kan ƴan Najeriya cikin sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel