Ana Daf da Gudanar da Zabe, ’Yan Bindiga Sun Harbe Jigon Dan Takarar PDP

Ana Daf da Gudanar da Zabe, ’Yan Bindiga Sun Harbe Jigon Dan Takarar PDP

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani dan takarar karamar hukuma a jihar Enugu da ke Kudancin kasar, Hon. Ejike Ugwueze
  • Marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyar Neke Odenigbo da ke karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar
  • Rundunar ‘yan sanda a jihar ta bakin kakakinta, DSP Daniel Ndukwe ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 8 ga watan Yuni

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu – ‘Yan bindiga sun bindige wani dan takarar shugabancin karamar hukuma a jam’iyyar PDP a jihar Enugu.

Marigayin mai suna Ejike Ugwueze ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ke tuki kan hanyar Neke Odenigbo a karamar hukumar Enugu ta Gabas.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

Yan bindiga sun hallaka dan takarar PDP a zabe
'Yan bindiga sun harbe dan takarar shugabancin karamar hukumar a jihar Enugu.
Asali: Original

Yaushe 'yan bindiga suka kashe dan PDP?

Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma’a 7 ga watan Yuni a yankin inda maharan suka zagaye shi tare da bindige shi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ugwueze mamban jam’iyyar PDP ne da ke neman takarar shugabancin karamar hukumar Isi-Uzo da ke jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a watan Oktoba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun tare motar dan siyasan kafin suka harbe shi nan take tare da tserewa.

Martanin wani kan kisan jigon PDP

Wani mazaunin yankin da ya bukaci boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana zargin kisan na da alaka da siyasa.

“Yana daga cikina gaba-gaba a cikin masu neman kujerar shugabancin karamar hukumar Isi-Uzo.”

Kara karanta wannan

Komai nisan jifa: Matashi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan shekaru da damfara

- Cewar majiyar

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 8 ga watan Yuni.

Ndukwe ya tabbatar da cewa yanzu haka jami’ansu suna ci gaba da bincike domin zakulo wadanda suka aikata laifin.

‘Yan bindiga sun sace matar sarki

A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da matar sarki a jihar Kaduna bayan kai wani hari.

Lamarin ya faru ne a yankin Ninzo da ke karamar hukumar Sanga a jihar inda suka kai farmaki fadar sarkin kafin aka dakile harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel