"Yadda Tinubu Yake Biyan Tallafin Fetur a Bayan Sanar da Soke Tsarin Tun Ranar Farko"

"Yadda Tinubu Yake Biyan Tallafin Fetur a Bayan Sanar da Soke Tsarin Tun Ranar Farko"

  • Atiku Abubakar ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya faɗawa ƴan Najeriya gaskiya game da biyan tallafin man fetur a gwamnatinsa
  • Wazirin Adamawa ya yi ikirarin cewa cire tallafi duk maganar baka ce, inda ya ce kuɗin tallafin bana 2024 ka iya kai wa N5.4trn
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce dama ya faɗi a baya cewa Tinubu ya dawo da tallafi a ɓoye ba tare da sanin ƴan ƙasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya daina yaudarar ‘yan Najeriya game da hakikanin matsayar gwamnatinsa kan tallafin man fetur.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya gitta, Allah ya yiwa babban jami'in ɗan sanda rasuwa yana zaune a ofis

Atiku da Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya yi ikirarin har yanzun ana biyan tallafin man fetur a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku ya yi iƙirarin gwamnatin Bola Tinubu na biyan makudan kuɗi a matsayin tallafin fetur ba tare da sanin ƴan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya cire tallafin fetur?

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya ce kuɗin da gwamnati ta biya da sunan tallafin mai karkashin mulkin Tinubu ka iya haura N5.4trn a bana (2024).

"A ranar rantsar da shi 29 ga watan Mayu, 2023, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur kuma tun lokacin gwamnatinsa take nanata cewa tallafin ya tafi.
"Wannan duk magace ta baki, na yi mamaki da naga labarin cewa har yanzun gwamnati tana biyan tallafi ba tare da sanin ƴan Najeriya ba."
"A sakona na cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya, na buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya yi bayani kan tallafin mai. Taya ake shigo da fetur kuma a rabawa ƴan kasuwa, a wane farashi?"

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga muhimmin taro kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Kuɗin tallafin fetur ya ƙaru a Najeriya

Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa har yanzu ana ware maƙudan kuɗi da sunan biyan tallafin mai fiye da lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

"A yanzu na san cewa kuɗin da aka kashe a tallafin mai ya kai N5.4trn a 2024, wanda ya zarce N3.6trn da aka ware a 2023, shekarar da Tinubu ya ce tallafin mai ya tafi."
"Biyan tallafi da yin karya a kai ba abin alfahari ba ne. Bai kamata ku yaudari ƴan Najeriya da wannan ba," in ji Atiku.

Gwamnati ta shiga taro da NLC, TUC

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya, ƙungiyoyin kwadago da kamfanoni masu zaman kansu sun sake shiga taro kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata

Rahoto ya nuna cewa wakilan gwamnatin tarayya a taron sun haɗa da ministan kuɗi, ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa da ministan kwaɗago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel