PDP Ta Watsawa Atiku Ƙasa a Ido Kan Hadaka da Kwankwaso, Obi, Ta Yi Alfahari
- Jam'iyyar PDP a Najeriya ta yi fatali da shirye-shiryen da Atiku Abubakar ke yi na haɗaka da sauran jam'iyyun adawa
- Jam'iyyar ta ce babu wani shiri da take yi a kan haka sai dai kofofinta a bude suke ga duk mai sha'awar shigowa cikinta
- Legit Hausa ta tattauna da wani ɗan PDP kan wannan sanarwar ta jam'iyyar ta fitar game da haɗaka da jam'iyyun adawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP mai hamayya ta yi martani kan jita-jitar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa a Najeriya.
Jam'iyyar ta nesanta kanta da labarin inda ta ce babu wannan maganar amma kofa a bude take ga duk mai son shigowa.
Jam'iyyar PDP ta bugi kirji kan karfinta
Wannnan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaran jami'yyar, Debo Ologunagba ya fitar a shafin Facebook a yau Laraba 5 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ologunagba ya bayyana yadda mutane ke tururuwa zuwa PDP inda ya ce hakan ya nuna jam'iyyar ce kadai zabin ƴan kasar a yanzu.
PDP ta ce kofofinta a bude suke
"Kwamitin gudanarwa na jam'iyya bayan ganawa ta 58 ya tabbatar da cewa PDP ba ta shirin haɗaka da jam'iyyun adawa."
"Sai dai ta ce a matsayin PDP na jam'iyyar al'umma, kofofinta a bude suke ga ƴan Najeriya da sauran mambobin da suka fice daga cikinta."
"PDP ta kasance jam'iyyar adawa mafi karfi wacce za ta iya cin zabe a Najeriya ba tare da magudi ba."
- Debo Ologunagba
Tattaunawar Legit Hausa da ɗan PDP
Legit Hausa ta tattauna da wani ɗan PDP game da wannan sanarwar ta jam'iyyar ta fitar kan haɗaka da jam'iyyun adawa.
Kwamred Abubakar Aliyu ya ce abin da ta fadi gaskiya ne amma siyasa ba ta yiwuwa sai da haɗakar jam'iyyun adawa kamar yadda APC ta yi.
"Lokaci ne zai tabbatar amma hadakar jamiyyun adawa yana da muhimmanci saboda haka APC ta yi wurin kwace mulkin PDP na tsawon shekaru."
"Taron neman haɗaka da jam'iyyun adawa ba matsala ba ne idan har hakan zai kawo nasara duk da matsalolin da ake samu a ciki."
- Abubakar Aliyu
Ya shawarci jam'iyyar da ta bude kofa ga duk wanda ke da sha'awar shiga ko neman haɗaka da ita domin samun nasara.
Atiku ya caccaki Tinubu kan tsare-tsarensa
Kun ji cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta azabtar da yan Najeriya cikin shekara daya.
Atiku Abubakar na cewa mulkin Tinubu ya zama kamar bulaliyar kan hanya wacce ba ta bar talaka da mai kudi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng