“A Gwada Matasa Kawai”: Tsohon Shugaban Kasa Ya Koka Kan Shugabancinsu

“A Gwada Matasa Kawai”: Tsohon Shugaban Kasa Ya Koka Kan Shugabancinsu

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasano ya nemo mafita ga rashin shugabanci da ake fama da shi a kasar
  • Obasanjo ya ce a yanzu lokaci ya yi da ya kamata a ba matasa sabbin jini dama domin samar da shugabanci mai inganci
  • Legit Hausa ta tattauna da wasu matasa kan wannan magana dangane da shugabancin matasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya koka kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya.

Obasanjo ya ce a yanzu kasar na bukatar sabbin jini domin ci gaba da gudanar da mulkin kasar tare da kawo sauyi a Najeriya.

Obasanjo ya bukaci kawo sabbin jini a shugabannin Najeriya
Olusegun Obasanjo ya ce dole a ba sabbin jini dama a mulkin Najeriya. Hoto: @officialABAT.
Asali: Twitter

Obasanjo ya bukaci ba matasa dama

Kara karanta wannan

Yayin da ake batun sauya tsarin mulki, Shettima ya fadi babban matsalar Najeriya

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka a jiya Asabar 1 ga watan Yuni yayin wani babban taro a jihar Lagos, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rashin tsaro ya gigita kasar tare da mayar da ita mafi hatsari da mutum zai yi rayuwa a cikinta bayan yunwa da matsin rayuwa, Punch ta tattaro.

“Zan ba da hanyoyi biyu kacal, dole mu tashi tsaye wurin kyankyasar sabbin jini da za su shugabanci kasar nan gaba.”
“Shugabanni masu tarbiya da kwarewa wadanda suka dauki mulii bautar jama’a ba bautar kansu ba.”
“A yadda Najeriya take a yanzu, kowa yana cikin hatsari ba za ka iya hasashen abin da zai faru a gobe ba.”

- OLusegun Obasanjo

Obasanjo ya bayyana illar rashin shugabanci

Obasanjo ya ce Najeriya tana da arzikin kasa wanda wasu kasashe kamar Japan da Singapore ba su da shi.

Kara karanta wannan

Za ka ji a jikinka": An bayyana jerin kalaman Jonathan ga Buhari kafin barin mulki

Sai dai ya ce duk tarun arziki da kasa ke da shi idan har babu shugabanci to babu inda wannan arziki zai yi amfani ga kasar.

Legit Hausa ya tattauna da wasu matasa

Legit Hausa ta tattauna da wasu matasa kan wannan magana dangane da shugabancin matasa

Kwamred Abdulkadir Abubakar ya ce tabbas matasa za su taka rawar gani idan suka samu dama.

Sai dai ya ce matasa da yawa sun samu dama amma ba su yi amfani da ita yadda ya dace ba.

Shugaban kungiyar matasa ta Youth Awareness Forum, Sani Adamu ya ce gaskiya lokaci ya yi da ya kamata a gwada su kamar yadda Obasanjo ya fada.

"Muna bukatar hakan amma da kamar wuya saboda mun dade muna neman a bamu amma har yanzu ba wani bayani."

- Sani Adamu

Obasanjo ya shawarci Tinubu kan tattalin arziki

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya kawo karshen matsalar tattalin arziki.

Obasanjo ya ce idan har ya gagara shawo kan matsalar zai iya tuntubar Zimbabwe da suka taba shiga irin wannan hali domin samun mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.