Shugaba Tinubu Ya Nuna Gwamna 1, Ya Buƙaci Sauran Gwamnoni Su Yi Koyi Da Shi

Shugaba Tinubu Ya Nuna Gwamna 1, Ya Buƙaci Sauran Gwamnoni Su Yi Koyi Da Shi

  • Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan su yi koyi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
  • Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta ya ce jikoki masu tasowa ba zasu manta da Gwamna Makinde ba
  • Ya ce gwamnan ya nuna yadda ake jagoranci da haɗa kan al'umma ta hanyar zuba ayyukan raya ƙasa da jawo kowa a jiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya kamata gwamnonin jihohin kasar nan su yi koyi da jagorancin Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Ya bayyana haka ne wurin kaddamar da babban titin tunawa da Adebayo wanda ya taso daga Alao zuwa Akala mai tsawon kilomita 76.7 a jihar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, jam'iyyar Kwankwaso ta aike da saƙo ga Bola Tinubu

Bola Tinubu da Gwamna Makinde.
Bola Tinubu yaba da salon shugabancin Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Seyi Makinde
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya yabi gwamnan Oyo

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya wakilci Bola Tinubu a wurin kaddamar da babban titin, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce waɗanda za su zo nan gaba za su yiwa gwamnan fatan alheri saboda dumbin ayyukan raya ƙasa da ya zubawa al'ummar jihar Oyo.

Meyasa gwamna Makinde ya zama abin koyi?

A kalamansa, Kashim Shettima ya ce:

"Gwamna Makinde, ƴaƴa da jikokin da za su zo nan gaba za su yi maka fatan alheri. Wannan ya zama abin koyi ga kowace jiha da duk wani dan Najeriya mai kishin ci gaban kasarmu.
"Mafi mahimmanci, ka nuna yadda ake shinfiɗa jagoranci na gari, ka yi ƙoƙarin haɗa kan al'umma ta hanyar jawo dattijon kasa, Janar Popoola ya shigo inuwarka.
“Na ga matan tsofaffin gwamnoni a nan, na ga tsofaffin mataimakan gwamnoni. Wannan shi ne abin da ake kira jagoranci, ka iya jan ragamar kowa da kowa domin gina gobe mai kyau."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kuɗin 2024 a majalisar tarayya

Gwamnan Oyo ya kusa kammala sabon titi

Gwamna Makinde, a lokacin da yake jawabi ya yi numi da cewa aikin titin Eruwa-Ido zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 48 zai kammala nan ba da jimawa ba.

Ya ce wannan wani ɓangare ne na kokarin da gwamnatinsa ke yi da nufin cike giɓin ayyukan more rayuwa a jihar Oyo, The Nation ta ruwaito.

TUC ta buɗewa Tinubu ƙofar sauƙi

A wani rahoton kuma an ji yan kwadago sun bayyana cewa za su iya rage adadin kuɗin da suke buƙatar a biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Shugaban TUC, Festus Osifo, ya ce gwamnatin tarayya ba da gaske take yi ba da ta gabatar da tayin N60,000 a taron ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel