2027: Tinubu Ya Yi Martani Kan Matsalar da Ya Ke Fuskanta Daga Haɗewar Atiku da Obi

2027: Tinubu Ya Yi Martani Kan Matsalar da Ya Ke Fuskanta Daga Haɗewar Atiku da Obi

  • Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan hadewar Atiku Abubakar da Peter Obi yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka inda ya ce ko kadan ba su damu da shirin jam'iyyun adawa ba
  • Idris ya ce a yanzu sun mayar da hankali ne kan yadda za su samar da ayyukan more rayuwa ga ƴan Najeriya madadin maganar zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya magantu kan hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya.

Idris ya ce ko kadan basu damu da duk wani shiri na jam'iyyun adawa ba saboda siyasa ta gaji haka.

Kara karanta wannan

Babban malamin Musulunci ya ja kunnen Ministar Tinubu kan hana aurar da mata a Niger

Tinubu ya magantu kan shirin hadewar Atiku da Obi kan zaben 2027
Gwamnatin Tarayya ta ce ko a jikinta game da shirin hadakar Atiku da Obi. Hoto: @Atiku.
Asali: Twitter

Tinubu ya yi martani kan Atiku, Obi

Ministan ya ce kowa yana da ra'ayin ya gana da kowa musamman a wannan tsari na dimukradiyya amma babu abin da ya shafe su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai tambayar da Ministan ya yi shi ne mene ya faru bayan ganawar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi, cewar rahoton Punch.

Ya ce ayyukan da Bola Tinubu ya yi na alheri sune za su tabbatar da nasararsa inda ya ce ƴan Najeriya sun fi son APC a yanzu fiye da lokacin zaben 2023.

Hankalin Tinubu ya koma kan ayyuka

"Gwamnati ba ta tunaninsu ko kadan, mun mayar da hankali ne kan yadda zamu sauke nauyin da aka daura mana."
"Ayyukan alheri da Tinubu ya ke yi sune abin da ya saka a gaba, kuma hakan ne abin da ƴan kasar ke bukata."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bayyana babbar matsalar dimokradiyya a Najeriya

"Bamu damu ba ko kadan, gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wurin samar da ayyukan more rayuwa ga ƴan kasa."

- Mohammed Idris

"Atiku, Obi za su taimaki Tinubu" - Onochie

A wani labarin, tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta magantu kan jita-jitar hadewar Atiku Abubakar da Peter Obi.

Onochie ta ce idan Atiku ya janyewa Obi, Shugaba Bola Tinubu zai samu nasarar lashe zabe cikin sauki a 2027.

Ta durkusa inda ta roki Ubangiji ya saka Atiku janyewa Peter Obi a zaben 2027 bayan ganawar da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel