"Shekara 1 da Na Yi Yafi 8 Ɗinka a Mulki": Gwamna Ya Sunce Zanin Mai Gidansa a Kasuwa

"Shekara 1 da Na Yi Yafi 8 Ɗinka a Mulki": Gwamna Ya Sunce Zanin Mai Gidansa a Kasuwa

  • Gwamna jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce ayyukan da ya gudanar a jihar yafi shekaru takwas na gwamnatin da ta shude
  • Fubara ya na magana ne kan gwamnan mai gidansa, Nyesom Wike inda ya ce ya kawo ayyukan alheri a cikin shekara daya kacal da ya yi
  • Wannan martani na zuwa ne yayin da rikicin siyasa jihar Rivers ke kara ƙamari tsakanin Wike da yaronsa, Gwamna Fubara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bugi kirji kan ayyukan alheri da ya yi a jihar.

Fubara ya ce ayyukan da ya yi a cikin shekara daya yafi na gwamnatin Nyesom Wike shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maidawa tsohon kwamishinansa martani, ya kira shi ‘dan kwaya a fili

Gwamna ya sake caccakar salon mulkin mai gidansa a siyasa
Gwamna Sim Fubara ya ce shekara 1 da ya yi a mulki yafi shekaru 8 na Nyesom Wike. Hoto: Government House Media, Rivers State.
Asali: Facebook

Rivers: Fubara ya bugi kirji kan ayyukan alheri

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da sabbin hanyoyi a yankin Ngo da ke karamar hukumar Andoni a jiya Asabar 18 ga watan Mayu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta wallafa faifan bidiyon YouTube yayin bikin inda ya ce ya daidaita komai tun farkon hawansa mukin da watanni uku duk da matsalolin siyasa a jihar.

Sakataren yada labaran gwamnan, Nelson Chukwudi ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai a jiya Asabar 18 ga watan Mayu.

Rriver: Rikici ya tilasta kwamishinoni yin murabus

Gwamna Fubara ya ce nan da watanni shida masu zuwa ƴan jihar za su yi gamo da ayyukan ci gaba masu muhimmanci.

Wannan na zuwa ne yayin da rikincin siyasa ke kara tsami tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Hakan ya jawo murabus din wasu kwamishinoni guda hudu a cikin mako daya wadanda ke goyon bayan Wike.

Wike ya ba da hakuri kan Fubara

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ba ƴan jihar hakuri kan kuskuren zaben Gwamnan Sim Fubara a matsayin magaji.

Wike ya ce wannan mataki da ya dauka na daga cikin nadamar da ya yi a rayuwarsa ta siyasa a jihar.

Ministan Abuja ya sha alwashin gyara kura-kuran da ya tafka a lokacin inda ya ce zai gyara su a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel