Atiku da Obi Na Shirin Haɗa Kai, Kungiya Ta Faɗi Wanda Ƴan Najeriya Za Su Zaɓa a 2027

Atiku da Obi Na Shirin Haɗa Kai, Kungiya Ta Faɗi Wanda Ƴan Najeriya Za Su Zaɓa a 2027

  • Ƙungiyar NPH mai goyon bayan APC ta mayar da martani kan yunkurin ƴan adawa na haɗa maja gabanin zaɓen 2027
  • Shugaban NPH, Hon. Bukie Okangbe ya ce babu wani kawance da ƴan siyasa za su ƙulla wanda zai kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓe na gaba
  • A cewarsa, ƴan Najeriya na tare da Bola Tinubu fiye da 2023 saboda sun fahimci manufofinsa na ceto ƙasar nan daga halin da ta shiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata ƙungiyar magoya bayan jam'iyyar APC (NPH) ta ce babu wata dabara ko maja da za a haɗa wadda za ta iya kayar da Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta ce matuƙar mambobin APC tun daga sama har ƙasa sun haɗa kansu, babu mai iya ganin bayan jam'iyyar a babban zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Atiku ya bayyana matsayarsa kan sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Wata ƙungiya ta ce babu mai iya kayar da APC a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarta, yadda jam'iyyun adawa suka fara ƙoƙarin haɗa kawance da ƴan siyasa ya nuna cewa akwai waɗanda suka shirya karawa da APC a 2027, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Najeriya sun aminta da Tinubu

Amma duk da haka ƙungiyar ta nuna kwarin guiwar cewa ƴan Najeriya na tare da APC fiye da yadda suka zaɓe ta a 2023 saboda suna jin daɗin mulkin Bola Tinubu.

Jagoran ƙungiyar NPH, Honorabul Bukie Okangbe ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja ranar Jumu'a.

Ya kuma yi kira ga dukkan magoya bayan APC da suka aminta da manufofin jam'iyyar su haɗa kai da jagorori domin samun gagarumar nasara a zaɓe na gaba.

Okangbe ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakin kusoshin APC, yana mai cewa akwai jan aiki a gabansu na sake lashe zaɓen 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

Haka nan kuma ya tabbatar wa Tinubu cewa ‘yan Najeriya na da kwarin gwiwa cewa zai iya dora kasar nan kan turbar tattalin arziki, tsaro da ci gaba, Vanguard ta ruwaito.

Okangbe ya bai mutane haƙuri

Mista Okangbe ya aminta da cewa mutane na fama da yunwa da wahalhalu amma ya roƙi ɗaukacin ƴan Najeriya su ƙara hakuri da Gwamnatin Tinubu.

"Shugaban ƙasa ya bai wa ƴan Najeriya haƙuri cewa wannan wahalar da ake sha ta wucin gadi ce kuma yana ƙoƙarin kawar da ita. Don haka ya kamata a ƙara haƙuri," in ji shi.

An taso Ganduje kan shugabancin APC

A wani rahoton kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da fuskantar adawa daga yankin Arewa ta Tsakiya.

Kungiyar ƴaƴan APC sun fara neman goyon baya domin kwato kujerar shugaban jam'iyyar APC daga hannun Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262