Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar Zamfara
- Jam'iyyar APC ta tabbatar da dakatar da ɗan majalisar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Honorabul Aminu Sani Jaji a jihar Zamfara
- Sakataren APC na jihar, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ya ce kwamitin zartarwa ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwa
- An ɗauki wannaan matakin ne bisa zargin Jaji da cin amanar jam'iyyar APC da kuma rashin mutunta gayyatar da aka yi masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Zamfara ta dakatara da ɗan majalisar wakilan tarayya, Aminu Sani Jaji.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin kan ɗan majalisar ne bisa zarginsa da cin amana da yi wa jam'iyya zagon ƙasa.
An dakatar da 'dan majalisa a APC
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Sani Jaji, shi ne mai wakiltar mazaɓar Kaura Namoda/Birnin Magaji a majalisar wakilai ta ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren APC na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ne ya sanar da haka yayin zantawa da manema labarai ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu.
Meyasa APC ta dakatar da Jaji?
Ibrahim Umar Dangaladim ya ce shugabannin jam'iyya na gundumarsa a Birnin Magaji sun dakatar da ɗan majalisar ne biyo bayan gano rashin gaskiyar da yake shukawa da rashin halartar tarurruka.
"Kwamitin ladabtarwa na mutum 7 ya bayar da shawarin a dakatar da shi saboda rashin mutunta gayyatar da kwamitin ya masa ba ɗaya ba kuma ba biyu.
"A halin yanzu kwamitin zartarwa na jiha ya yi nazari kan rahoton kwamitin ladabtarwa kuma ya amince da shawarwarin ɗaukar matakin dakatar da ɗan majalisar.
"Duba da haka, kwamitin zartarwa na APC ta jihar Zamfara ya amince da dakatar da Honorabul Aminu Sani Jaji daga jam'iyyar."
- Ibrahim Umar Dangaladima
Wannan dai ya ƙara tabbatar da matakin da jam'iyyar APC reshen Birnin Magaji ta ɗauka kan Aminu Sani Jaji, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto
Jigon PDP ya koma APC a Osun
A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP a jihar Osun a karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta rasa ɗaya daga cikin manyan kusoshinta
Alhaji Shuaib Oyedokun ya fice daga PDP kamar yadda ya bayyana a wasiƙar da ya miƙa wa shugannin jam'iyyar na Osun ranar Alhamis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng