Siyasar 2027: Ka Yi Hankali Da Mutanen Arewa, Ibo Sun Fara Gargadin Peter Obi

Siyasar 2027: Ka Yi Hankali Da Mutanen Arewa, Ibo Sun Fara Gargadin Peter Obi

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta gargadi dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023, Peter Obi da ya guji mannewa Arewa a kokarinsa na neman kuri'a
  • A kwanakin nan, ana ganin Peter Obi na yawan mu'amala da jagororin Arewa ciki har da tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar
  • Kungiyar ta Ohanaeze ta ce ya kamata Peter Obi ya dauki darasi daga tsofaffin 'yan takarar shugabancin kasar nan da su ka fito daga yankin Ibo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Kungiyar Kabilar Ibo ta Ohanaeze ta gargadi tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin inuwar jam'iyyar Labor Party da ya yi hankali da 'yan Arewa a kokarin da ya ke na samun nasara a kakar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa ya tsananta, Izala ta umarci masallatai a fara Al-kunut

Tsagin Chidi Abeh ne ya ba wa Peter Obi shawarar, inda ya bayyana cewa sun lura da yadda dan takarar ya matsa da kai ziyara ga daidaikun shugabanni a Arewacin kasar nan, da ma halartar tarukan musulmi.

Peter Obi
2027: kungiyar Ohanaeeze ta gargadi Peter Obi ya yi hankali da Arewa Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta nuna cewa akwai alamun Peter Obi na kokarin hadewa da wasu wajen kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaben 2027, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Peter Obi ya dauki darasi," Ohanaeze

Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze ta shawarci dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya dauki darasi daga wasu 'yan kabilar Ibo da su ka tsaya takara irin tasa a baya, kamar su Ogbonnaya Onu, Rochas Okorocha da Chuba Okadigbo.

Kungiyar ta bayyana cewa shishshigewa 'yan Arewa da ya ke yi ba zai kai shi ga samun nasara ba domin 'yan Arewa na da wani kulli a zuciyarsu game da shi, kamar yadda Punch News ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Buhun shinkafa da atamfa kawai aka raba mana bayan zabe," shugabannin matan APC

Ohanaeze ta shawarci Peter Obi da ka da ya raja'a da 'yan Arewa kadai, kuma ya rika mu'amalantarsu a matakin shiyya maimaikon neman goyon baya daga daidaikun jama'a.

Ohanaeze tayi watsi da maganar Atiku

A baya mun ba ku labarin cewa kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze ta ki amincewa da shawarar mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na yin wa'adai daya kacal a kan mulkin kasar nan.

Kungiyar na ganin wannan dabara ce ta tsohon mataiamakin shugaban kasar da zai hana su cimma muradin neman shugabancin kasar nan, wanda su ka ce ba zai yiwu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel