Shugaban Inyamuran Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor, ya mutu

Shugaban Inyamuran Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor, ya mutu

  • Al'ummar Igbo a Najeriya sun yi rashin babban 'dansu kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo
  • Obiozor ya kasance tsohon Ambasadan Najeriya zuwa kasar Amurka da kasar Isra'ila
  • Marigayin ya mutu ne bayan shekaru uku da zabensa a matsayin shugaban Ohanaze Ndigbo Janar

Owerri - Shugaban kungiyar kare muradun yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor, ya rigamu gidan gaskiya.

Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya sanar da mutuwar Obiozor a jawabin da fadar gwamnatin jihar ta fitar da daren Laraba, rahoton Vanguard.

Obiozor
Shugaban Inyamuran Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor, ya mutu Hoto: Presidency
Asali: Twitter

A cewar jawabin;

"A madadin gwamnati da al'ummar jihar Imo, ni Sanata Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, na alhinin sanar da mutuwar babban 'danmu jihar nan kuma Najeriya, Shugaban Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan PDP Ya Ce Bola Tinubu Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

"Babban dan Bokon, jajirtaccen dan Diflomasiyya, dan kasa, George Obiozor, ya mutu ne bayan gajeruwar jinya da yayi."
"Mutuwar shugaban Inyamurai kuma tsohon Jakadan Najeriya zuwa Amurka da kasar Isra'ila babban rashi ne ga Najeriya , jihar Imo, Arewa maso gabashin Najeriya."
"Ko shakka babu Najeriya da kasashen waje zasu yi rashinsa bisa iliminsa da shawarin da yake badawa."

Jawabin ya kara da cewa iyalansa zasu sanar da yadda za'a shirya jana'izarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel