Kwamishina Na 4 Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Tura Wasiƙa Ga Gwamna Fubara
- Jacobson Nbina, kwamishinan sufuri a jihar Ribas ya yi murabus daga muƙaminsa a wata takarda da ya aike wa Gwamna Fubara ranar Laraba
- Mista Nbina ya zama mutum na hudu daga cikin kwamishinonin gwamnatin Ribas da suka aje aiki a daidai lokacin da rikicin siyasa ya ƙara tsananta
- Jihar Ribas ta faɗa cikin rigingimun siyasa ne tun bayan lokacin da aka samu saɓani tsakanin Gwamna Simi Fubara da uban gidansa, Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Kwamishinan sufuri na jihar Ribas, Jacobson Nbina, ya yi murabus daga muƙaminsa na mamba a majalisar zartarwar jihar.
Wannan mataki da ya ɗauka ya sa adadin kwamishinonin da suka yi murabus a gwamnatin Siminalayi Fubara ya zama huɗu zuwa yanzu.
Rigimar gwamna Fubara da Nyesom Wike
Mista Nbina, na ɗaya daga cikin kwamishinonin Gwamna Fubara da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Nation ta tattaro, Nbina ya tabbatar da murabus daga muƙamin ne a wata takarda da ya aike wa Gwamna Fubara ta ofishin sakataren gwamnatin Ribas, Tammy Danagogo.
Kwamishinonin da suka yi murabus a Rivers
Tun farko dai kun ji cewa kwamishinan ilimi na jihar Ribas, Farfesa Chinedu Mmon, ya aje aiki a gwamnatin Fubara saboda wahalar aikin.
A wasiƙar da ya aika wa SSG, Farfesa Mmon ya ce dalilin yin murabus dinsa shi ne saboda aiki a karkashin gwamna ya zama abu mai wahala.
Msita Gift Worlu, kwamishinan gidaje a jihar Ribas shi ma ya yi murabus daga gwamnatin Fubara. Ya ce wannan matakin na ɗaya daga ciki mafi wahala da ya ɗauka a rayuwarsa.
Haka zalika kwamishinan mahalli, Honorabul Austin Ben-Chioma, ya bi sahun ƴan uwansa, ya yi murabus daga majalisar zartarwar jihar Ribas.
Dalilin dai iri ɗaya ne da sauran, murabus din Ben-Chioma ya zo ne a daidai lokacin da rikicin siyasar jihar ke ƙara zafi tsakanin tsagin Wike da Gwamna Fubara.
Fubara ya caccaki Wike kan bashi
A wani rahoton kuma Gwamna Siminalayi Fubara ya zargi tsohuwar gwamnatin da Nyesom Wike ya jagoranta da tarawa jihar Ribas tilin bashi.
Gwamnan ya bayyana cewa yanzu haka 'yan kwangila sun addabi gwamnatinsa da neman cikon kudin aikin da suka aiwatar a kan bashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng