"Ban da Hannu": Ɗan El-Rufai Ya Faɗi Gaskiya Kan Kwangiloli a Mulkin Mahaifinsa a Kaduna

"Ban da Hannu": Ɗan El-Rufai Ya Faɗi Gaskiya Kan Kwangiloli a Mulkin Mahaifinsa a Kaduna

  • Bello El-Rufai ya bayyana cewa babu hannunsa ko kaɗan a rabon kwangiloli a tsohuwar gwamnatin Kaduna karkashin mahaifinsa
  • Ɗan majalisar tarayyan ya ce tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai mutumin kirki ne wanda Najeriya ke buƙata a matsayin shugaba
  • Ya ce da shi aka yi kamfe a lokacin da mahaifinsa ke neman zama gwamnan Kaduna amma bayan an ci zaɓe aka nesanta shi da gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilan tarayya, Bello El-Rufai'i ya ce bai taɓa karɓan kwangila a mulkin mahaifinsa ba.

Bello, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai,ya ce ba ruwansa da harkokkn ba da kwangila a tsohuwar gwamnatin da ta gabata a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N19.4bn: An samu matsala yayin gurfunar da Ministan Buhari da ɗan uwansa a kotu

Bello El-Rufai.
Bello El-Rufai ya nesanta kansa daga hannu a rabon kwangiloli a mulkin mahaifinsa Hoto: Bello El-Rufai
Asali: Twitter

Ɗan majalisar tarayyar ya bayyana haka ne a wata hira da Yaya Abba ya shirya mai taken ‘Tare da Shuraim’, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muƙaman da El-Rufai ya riƙe a gwamnati

Malam Nasir El-Rufai ya rike mukamin ministan babban birnin tarayya daga shekarar 2003 zuwa 2007 a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Bayan haka, ya zama gwamnan jihar Kaduna na tsawon zango biyu daga 2015 zuwa 2023, rahoton Naija News.

Kwanan nan aka zarge shi da bar wa magajinsa, Malam Uba Sani tulin bashi da ya kai Dala miliyan 587, N85bn, da kuma N115bn na kwangila.

Gwamna Uba Sani ya ce bashi ya yi wa Kaduna katutu kuma ƴan kuɗaɗen shigar da take samu kaɗai ba su kai a biya ma'aikata albashi ba.

Shin ana ba Bello kwangila a mulkin El-Rufai?

Kara karanta wannan

Jita-jita ta yawaita yayin da Peter Obi ya gana da tsohon gwamnan jihar Jigawa

Da yake jawabi, Bello El-Rufai ya ce:

"Ina ganin shi (Malam Nasir) mutum ne na kwarai kuma irin shugaban da Nijeriya ke bukata, akwai mutane da yawa kamarsa. Mun masa kamfe sosai.
"Amma yana zama gwamna ya tura ni gefe, kamar yadda na ce, na yi hijira. Ba kamar ’ya’yan gwamnoni a lokacin ba, a gaskiya ban zauna a Kaduna ina yin kwangiloli ba."

Yayin da yake bayyana cewa yanzu ya fahimci dalilin da ya sa mahaifinsa ya yanke shawarar tsame shi daga fagen siyasa a lokacin, Bello ya ce:

"Abin da ke faruwa da wanda ke kan mulki shi ne idan suka gaza tunkararsa kai tsaye, sai su lallaɓa wurin matansa ko ƴaƴansa. Haka ƴan kwangila suke a Kaduna, suna tunanin idan suna bi ta hannunka za a masu alfarma."
"Ya tsame ni gaba ɗaya daga lissafin mulki kuma hakan ya taimaka sosai."

An fasa auren marayu 100 a Niger

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya yi rashin nasara a babbar kotun tarayya

A wani labarin kuma kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ya soke shirin aurar da marayun ƴan mata 100.

Sarkindaji ya bayyana cewa ya haƙura ya bar wa ministar harkokin mata ta ɗauki nauyin su, inda ya ce ta wuce gona da iri kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel