Matsala Ga Tinubu Yayin da Atiku Abubakar Ya Gana da Peter Obi, Bayanai Sun Fito
- Manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027
- Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi
- Wannan ziyara na zuwa ne bayan kakakin Atiku ya bayyana alamar cewa da yiwuwar manyan ƴan siyasar biyu su haɗa kansu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Manyan ƴan siyasa na ci gaba da shirye-shirye yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya.
Rahoton da ya shigo mana na nuni da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci takawaransa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ne ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar ya ce abin alfahari ne a gare shi da ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.
Sai dai Atiku bai bayyana cikakken bayani kan abin da ya tattauna da Mista Obi yayin wannan ziyara ba.
Wannan ganawa ta manyan siyasar biyu na zuwa ne bayan mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya nuna alamun cewa ƴan siyasar biyu na iya haɗewa.
'Wike ne ya kori Obi daga PDP'
Idan ba ku manta ba Obi ne abokin takarar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2019 karkashiin inuwar PDP amma daga baya tsohon gwamnan ya fice zuwa LP gabanin zaɓen 2023.
A wata hira, Mista Ibe ya ce babu ruwan Atiku a sauya sheƙar Peter Obi, inda ya ƙara cewa tsohon gwamnan Ribas kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ne ke da laifi.
A cewar Paul Ibe, Atiku ya amince da tsarin karɓa-karba amma ya kafe sai dai a kai tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa shiyyar Kudu maso Gabas.
Ya ce amma Wike ya ɓata tsarin da cewa sai dai a miƙa tikitin Kudu gaba ɗaya, shiyasa Atiku ya shiga takara kuma ya samu nasara.
Wani jigon PDP kuma ɗan amutun Atiku, Muhammad Kabir, ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa dama Obi da Kwankwaso ne suka hana Atiku lashe zaɓen 2023.
Ya ce yana ɗaya daga cikin waɗanda ke takaicin matakin Peter Obi na barin PDP, wanda a cewarsa shi ne babban abin da ya kayar da jam'iyyar.
"Muna maraba da shi idan zai dawo PDP, dama idan ka duba zaɓen 2019, Atiku da Ibi ne ƴan takarar PDP, ya kake tunani da ace suna tare da 2023?"
"Wannan ziyara abu ne mai kyau kuma muna fatan har Kwankwaso ya zo ya haɗa kai da wazirin Adamawa su kawo mana ƙarshen wannan mulkin," in ji shi.
Tinubu ya jagoranci taron FEC
A wani rahoton kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa (FEC) karo na biyar a 2024 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin
Gabanin fara taron, majalisar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama tsofaffin ministoci biyu da suka kwanta dama.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng