Kotu Ta Kori Ƴan Majalisa 27 da Suka Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ta Hana Su Aikin Majalisa

Kotu Ta Kori Ƴan Majalisa 27 da Suka Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ta Hana Su Aikin Majalisa

  • Ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja sun shiga matsala yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ya dawo ɗanye
  • Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar Ribas har sai ta yanke hukunci
  • Mambobin majallisar da wannan umarni ya shafa sune waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a lokacin rigimar Wike da Fubara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Rikicin siyasar jihar Ribas ya ƙara ƙamari yayin da babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta kori ƴan majalisa 27 masu goyon bayan ministan Abuja.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa babbar kotun ta hana mambobi 27 na majalisar dokokin jihar Ribas daga bayyana kansu a matsayin halastattun ƴan majalisa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana dalilin da ya sa suka mamaye gidajen ƴan majalisu a Fatakwal

Kotu ta yanke hukunci kan ƴan majalisar Wike.
Babbar kotun Ribas ta haramtawa ƴan majalisa 27 na tsagin Wike ayyana kansu a matsayin mambobin majalisa Hoto: Rivers State House of Assembly
Asali: UGC

Mai shari'a Charles N. Wali ne ya ba da wannan umarnin ranar Jumu'a 10 ga watan Mayu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya bayyana cewa kujerun ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC sun zama babu kowa har sai kotu ta yanke hukuncin ƙarshe.

Meyasa kotu ta ɗauki wannan matakin?

Kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, da sauran mambobi 26 da wannan umarni ya shafa suna tare ne da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Sun tattara sun sauya sheƙa zuwa All Progressives Congress (APC) a lokacin da faɗan Wike da Gwamna Siminalayi Fubari ya yi zafi.

Bayan sun sauya sheƙa ne kuma aka ayyana kujerunsu a matsayin waɗanda babu kowa.

Ƴan majalisa 27 sun faɗa matsala

Waɗanda ake ƙara sun haɗa da Gwamna Fubara, Antoni Janar na jihar da kuma ƴan majalisa 27 masu goyoj bayan Wike.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe babban malamin Musulunci da wasu mutum 30 a Zamfara

Kakakin majalisar dokokin Ribas na tsagin Gwamna Fubara, Oko-Jumbo da wasu mutum biyu ne suka shigar da wannam ƙara a gaban kotu.

Kotun ta kuma hana ‘yan majalisar yin taro da zama a a babban dakin taro na majalisar dokokin da ke kan titin Aba, Fatakwal.

Haka nan kuma ta hana ƴan majlaisar zama a kowane wuri da nufin yin ayyukan majalisar dokokin jihar Ribas, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Fubara ya hana ciyamomi zuwa majalisa

A wani rahoton kuma Gwamna Simi Fubara ya hana ciyamomi da dukkan jagororin kananan hukumomi 23 bayyana a gaban majalisar dokokin Ribas.

Wannan mataki na zuwa ne awanni 24 bayan APC ta umurci majalisar ta fara shirin tsige Fubara daga kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262