Duk da Kokarin Tinubu, Rikicin Wike da Fubara Ya Sake Munana Bayan Matakin Majalisa

Duk da Kokarin Tinubu, Rikicin Wike da Fubara Ya Sake Munana Bayan Matakin Majalisa

  • Dukkan kokarin sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya yi a rikicin siyasar Rivers ya ci tura bayan zaben sabon shugaban Majalisar a yau
  • An nada sabon shugaban tsagin Majalisar jihar, Victor Oko Jumbo a yau Laraba 8 ga watan Mayu a matsayin shugabanta
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake takun saka tsakanin gwamnan Siminalayi Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Rikicin siyasar Rivers ta sauya salo bayan rantsar da sabon shugaban Majalisa.

An nada Victor Oko Jumbo wanda ke wakiltar mazabar Bony a jihar Rivers a matsayin shugaban tsagi na Majalisar.

Bayan kokarin Tinubu, rikicin Wike da Fubara ya sake dagulewa a Rivers
Rikicin Wike da Fubara ya rincaɓe a Rivers duk da kokarin sulhu Daga Bola Tinubu. Hoto: @IBOGENERAL3, @GovWike, @SimFubaraKSC.
Asali: Twitter

Rikicin Wike, Fubara ya ƙi ƙarewa

Kara karanta wannan

Harajin CBN: Na hannun daman Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi

Wannan mataki na zaben sabon shugaban Majalisar ya lalata kokarin sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da rikicin siyasar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan takun saka tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike, cewar The Nation.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a tabbatar ko an gudanar da zaben Jumbo a matsayin shugaban 'yan taware a majalisar ba.

An nada na hannun daman Fubara

Jumbo wanda na hannun daman Gwamna Fubara ne ya maye gurbin tsohon shugaban Majalisar, Edison Ehie, Leadership ta tattaro wannan.

Ehie wanda ke tare da Fubara ya yi murabus daga mukaminsa da kuma Majalisar gaba daya a ranar 31 ga watan Disambar 2023.

Daga bisani gwamnan ya nada Ehie a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna ya ɗauki zafi yayin da APC ta umurci majalisa ta tsige shi nan take

Wannan na zuwa ne bayan kokarin da Shugaba Tinubu ya yi a watan Disambar 2023 domin sasanta rikicin mai gidan da yaronsa.

Fubara ya fusata kan shirin tsige shi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ɗauki zafi yayin da rikici ya dawo ɗanye tsakaninsa da majalisar dokokin jihar.

Fubara ya sanar da haramtawa dukkan ciyamomi da manyan jami'ai a kananan hukumomin jihar zuwa gaban majalisar musamman mai goyon bayan Nyesom Wike.

Har ila yau, gwamnan ya yi barazanar tsige dukkan wani shugaban karamar hukuma da ya zo gaban Majalisar a yau Laraba 8 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.